Shagari Zuwa Buhari: Lokuta 9 da Aka Rantsar da Shugabannin Kasa a Tarihin Najeriya

Shagari Zuwa Buhari: Lokuta 9 da Aka Rantsar da Shugabannin Kasa a Tarihin Najeriya

  • A ranar yau, 29 ga watan Mayun 2023, za a samu canjin mulki daga tsoho zuwa sabon shugaban kasa
  • Bola Ahmed Tinubu zai karbi ragamar shugabancin Najeriya a hannun Shugaba Muhammadu Buhari
  • Kafin yanzu, an rantsar da shugabannin farar hula daga Oktoban shekarar 1979 zuwa yau a Najeriya

Abuja - Ganin ana bikin rantsar da sabon shugaban kasa a Najeriya, rahoton nan ya tuna da baya, ya dauko lokutan da aka yi irin haka a baya a tarihi.

1. Alhaji Shehu Shagari - 1979

Mutumin farko da aka fara rantsarwa a matsayin shugaban kasa a salon mulkin nan shi ne Shehu Usman Aliyu Shagari, wanda aka yi bikin hawansa mulki a ranar 1 ga watan Oktoba, 1979.

An yi biki ne a filin Tafawa Balewa da ke Legas, inda Mai shari’a Atanda Fatai Williams ya rantsar da shi.

Olusegun Obasanjo
Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Eagle Square Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Alhaji Shehu Shagari (Tazarce) - 1983

Bayan shekaru hudu sai aka sake rantsar da Shehu Shagari a sakamakon nasarar da ya samu a zaben 1983. A wannan farfajiya dai aka sake yin bikin da ya zama na karshe a garin Legas.

3. Olusegun Obasanjo - 1999

Bayan shekaru 20 da mika mulki ga farar hula, sai aka rantsar da Janar Olusegun Obasanjo (mai ritaya), wannan karo a matsayin zababben shugaban kasa da ya lashe zabe a 1999.

Wannan karo Obasanjo ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu. Alkalin Alkalai, Mohammed Lawal Uwais ya rantsar da shi a filin Eagle Square da ke sabuwar birnin tarayya na Abuja.

4. Olusegun Obasanjo (Tazarce) - 2003

Kamar yadda aka rantsar da shi a karon farko, haka Olusegun Obasanjo ya dawo filin Eagle Square domin ya fara wa’adinsa na biyu a sakamakon nasara da ya yi a zaben tazarce.

5. Umaru Musa Yar'Adua - 2007

Ranar 29 ga watan Mayun 2007 ya zama karon farko a tarihi da aka canza gwamnati a mulkin farar hula, Alkalin Alkalai, Idris Legbo Kutigi ya rantsar da Umaru Musa Yar'Adua.

Sai dai Shugaba Umaru Musa Yar'Adua bai cika wa’adinsa ba, rai ya yi halinsa a shekarar 2010.

6. Goodluck Jonathan - 2010

A ranar 6 ga watan Mayun 2010 sai Mai shari’a Justice Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu ya rantsar da mataimakin shugaban kasa, Goodluck Jonathan a matsayin shugaban Najeriya.

7. Goodluck Jonathan (Zabe) - 2011

Bayan ya kare wa’adin tsohon mai gidansa, sai Goodluck Jonathan ya shiga zabe a 2011 kuma ya yi nasara don haka Alkalin Alkalai ya kuma rantsar da shi a filin Eagle Square a Abuja.

8. Muhammadu Buhari - 2015

A 2015 aka sake kafa tarihi a Najeriya, jam’iyyar adawa ta karbe mulki a zabe. A ranar 29 ga watan Mayu Alkalin Alkalai Mahmud Mohammed ya rantsar da Muhammadu Buhari.

9. Muhammadu Buhari (Tazarce) - 2023

Bayan an sake yin zabe a 2023, Mai girma Buhari ya sake yin nasara. Wannan karo Ibrahim Tanko ya rantsar da shugaban a bikin rantsuwa na bakwai da aka yi a Eagle Squre.

Wanene Bola Tinubu

Kun samu rahoto dauke da tarihin Bola Tinubu, wanda gogaggen dan siyasa ne kuma jagora wanda ya hidimatawa kasarsa a bangarori dabam-dabam.

Sabon shugaban kasar ya yi gwamna a jihar Legas tsakanin Mayun 1999 zuwa Mayun 2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel