Iyalina Ba Su Bukatar Dukiyar Najeriya Domin Mu Rayu Inji Mai Dakin Bola Tinubu

Iyalina Ba Su Bukatar Dukiyar Najeriya Domin Mu Rayu Inji Mai Dakin Bola Tinubu

  • Remi Tinubu ta ce ba su bukatar taba baitul-mali, ta yi alkawarin gwamnatinsu za ta gyara kasa
  • Uwargidar Shugaban Najeriyar ta ce Mai gidanta ya na bukatar addu’o’i da falalar Ubangiji a ofis
  • Bola Tinubu ya zama shugaban kasa a shekaru 71, mai dakinsa ta ce tana shirin cika shekara 63

Abuja - A karshen makon jiya ne aka ji matar sabon shugaban Najeriya, Remi Tinubu ta ce danginta ba su bukatar dukiyar Najeriya domin su rayu.

Vanguard ta rahoto Sanata Remi Tinubu ta na cewa abin da mai gidanta, Bola Ahmed Tinubu yake bukata shi ne falalar Ubangiji wajen shugabanci.

‘Yar siyasar wanda Fasto ce, ta nuna cewa su na bukatar addu’o’in mutanen Najeriya yayin da ta ce gwamatin Tinubu za ta yi abin da ya kamata.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya na rantsuwa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A jawabin da tayi a babban cocin kasa, Sanatar mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawa ta ce baitul-malin Najeriya na ‘yan kasa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan nasarar da mai gidanta ya samu a zaben shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta ce lokaci ya yi yanzu da za a hada-kan al’ummar Najeriya.

Ba su taba tunani ba

Ubangiji ya nuna mana rahamarsa. Zan iya fada maku cewa ba mu tunanin hakan za ta faru ba. Amma mun gode da Ubangiji ya ba mu kwarin gwiwa, ya ba mu karfin jajircewar cigaba da fadin-tashin rayuwa.
Shekarar Asiwaju 71, ni kuma zan cika 63. Ina ganin zan zama cikin mafi tsufan uwargidar shugaban Najeriya da aka taba yi.

- Remi Tinubu

Punch ta rahoto tsohuwar uwargidar jihar Legas ta na cewa irin ikon da Ubangiji ya yi a ranar zaben fitar da gwani, shi ya maimatu a yanzu.

"Dukiya mallakar kowa ce"

Mu na bukatar falalar Ubangiji kuma mu na bukatar mu yi abin da ‘Yan Najeriya su ke buri.
Dukiyar Najeriya arzikin kowane ‘dan kasa ne. Mallakar kowa ce. Ubangiji ya azurta dangi na.
Ba mu bukatar dukiyar Najeriya domin mu rayu sai dai mu yi abin da ya dace. Kuma na yi maku alkawari a cocin nan, da taimakonku, za mu gyara kasar nan.

- Remi Tinubu

Abubuwa 7 da Tinubu ya fada

Kamar yadda aka ji tun tuni, babu maganar tallafin fetur a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. An rahoto sabon shugaban kasar ya tabbatar da haka.

Sannan Gwamnatin Bola Tinubu za ta waiwayi canjin kudi da sauran tsare-tsaren babban bankin CBN kuma jami’an tsaro za su samu horo da kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel