Ba Jira: Gwamna Abba Ya Nada Sabuwar Shugabar Hukumar PCACC a Kano
- Gwamnan Kano Abba Yusuf ya naɗa Barr. Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar riƙon kwarya ta hukumar PCACC ta jihar
- Kafin naɗin, Kutama ita ce sakatariyar Hukumar Karbar Korafe-Korafen Jama'a da Yaƙi da Rashawa ta jihar Kano
- Naɗin ya biyo bayan rahoton murabus ɗin shugaban hukumar, Saidu Yahaya, da kuma sukar da gwamnan ya yi kan ayyukan hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Barr. Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar riƙon kwarya ta Hukumar Korafe-Korafen Jama'a da Yaƙi da Rashawa ta jihar (PCACC).
Gwamna Abba ya ba sabuwar shugabar hukumar mukamin ne biyo bayan murabus din da tsohon shugabanta ya yi.

Source: Facebook
Mai ba Gwamnan Kano shawara kan kafafen sada zumunta na zamani, Ibrahim Adam, ne ya sanar da naɗin a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 16 ga watan Satumban 2026.
Hafsat Kutama ta kasance sakatariyar hukumar Ibrahim ya ce Kutama ta kasance sakatariyar hukumar kafin Gwamna Abba Yusuf ya naɗa ta shugabar riƙon kwarya.
A cikin sanarwar, ya ce:
“Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Barr. Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar riƙon kwarya ta Hukumar Korafe-Korafen Jama'a da Yaƙi da Rashawa (PCACC) ta Jihar Kano.”
Ya ƙara da cewa:
“Kafin naɗin nata, Barr. Hafsat ta kasance Sakatariyar Hukumar.”
Shugaban hukumar PCACC ya yi murabus
Naɗin Barr. Hafsat Kutama ya zo ne bayan rahoton cewa tsohon shugaban hukumar, Saidu Yahaya, ya yi murabus daga muƙaminsa ranar Talata, 15 ga Satumba, 2026.
Saidu Yahaya ya karɓi shugabancin PCACC ne a watan Agustan 2025, bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Rimin Gado.
Abba Yusuf ya soki ayyukan hukumar
Jaridar Daily Trust ta ce murabus dinsa ya biyo bayan kalaman Gwamna Abba Yusuf na baya-bayan nan, inda ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda hukumar ke gudanar da aikinta a ƙarƙashin jagorancinsa.
Gwamnan ya taɓa ƙalubalantar shugaban hukumar a bainar jama’a da ya ƙara kaimi wajen yaƙi da rashawa. Abba Kabir Yusuf ya kuma gargaɗi duk wanda ba ya son sauke nauyin da aka ɗora masa da ya sauka daga mukaminsa.
Gwamnan na son hukumar ta ƙara zage damtse
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma bayyana fatan cewa PCACC za ta sake samun tasirinta wajen yaƙi da rashawa a jihar.
Ya ce yana son hukumar ta ƙara zage damtse wajen magance matsalar rashawa da kuma tabbatar da cewa jami’an gwamnati suna ɗaukar alhakin ayyukansu.

Source: Facebook
Kwankwasiyya ta zargi Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamma Abba Kabir Yusuf da muzgunawa yan adawa.
Magoya bayan na dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso sun kuma zargi gwamnatin Abba da hana yan Majalisar jam'iyyun adawa gudanar da ayyukansu.
Asali: Legit.ng

