Rantsar da Tinubu: Jerin Shugabannin Kasa Da Suka Gabata Da Yadda Suka Samu Nasara a Zabe

Rantsar da Tinubu: Jerin Shugabannin Kasa Da Suka Gabata Da Yadda Suka Samu Nasara a Zabe

Abuja - Najeriya ta yi sabon shugaban ƙasa a ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023, bayan an rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sabon shugaban ƙasa a dandalin Eagles Square, da ke Abuja.

Legit.ng ta yi duba kan yadda sauran shugabannin ƙasa da suka gabata, suka samu nasara a zaɓensu tun daga shekarar 1979.

Jerin tsaffin shugabannin Najeriya da aka zaba
Tsaffin shugabannin Najeriya da aka zaba Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Zaɓen 1979: Yadda Shehu Shagari ya samu nasara

An yi zaɓen shugaban ƙasa na farko a Najeriya a ranar 11 ga watan Agustan 1979. Ɗan takarar jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN) Shehu Shagari, ya lashe zaɓen da ƙuri'u 5,688,857.

Obafemi Awolowo na jam'iyyar Unity Party of Nigeria (UPN) ya zo na biyu inda ya samu ƙuri'u 4,916,551, sannan Nnamdi Azikiwe na jam'iyyar Nigerian People's Party (NPP) ya zo na uku inda ya samu ƙuri'u 2,822,523.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Muhimman Abubuwa 3 Da Yakamata Ku Sanya Ido Akai a Ranar 29 Ga Watan Mayu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zaɓen 1983: Shehu Shagari ya sake yin nasara

An gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na wannan shekarar a ranar 6 ga watan Agustan 1983. Shugaban ƙasa mai ci a lokacin Shehu Shagari, ya samu ƙuri'u 12,081,471 inda ya yi nasara a jihohi 11 da kaso 47.51%.

Awolowo na jam'iyyar UPN ya samu ƙuri'u 7,907,20, inda ya yi nasara a jihohi biyar da kaso 31.09%. Jam'iyyar NPP ta samu ƙuri'u 3,557,113 inda ta yi nasara a jihohi biyu da kaso 13.99%.

Zaɓen shugaban ƙasa na 1999: Yadda Obasanjo ya samu nasara

Bayan an dawo mulkin dimokuraɗiyya, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Olusegun Obasanjo, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya zama shugaban ƙasa a 1999 bayan ya samu ƙuri'u 18,738,154, inda ya samu kaso 62.8% na yawan ƙuri'un.

Cif Olu Falae na jam'iyyar Alliance For Democracy (AD), ya zo na biyu inda ya samu ƙuri'u 11,110,287, wanda hakan na nufin ya samu kaso 37.2% na yawan ƙuri'un.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimmin Abinda Ya Sauya a Najeriya Daga 2015 Zuwa 2023

Zaɓen shugaban ƙasa na 2003: Obasanjo ya yi tazarce

An gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 2003 a ranar 19 ga watan Afirilu, inda Obasanjo na jam'iyyar PDP ya yi nasara da ƙuri'u 24,456,140.

Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) ya zo na biyu inda ya samu ƙuri'u 2,710,022.

Zaɓen shugaban ƙasa na 2007: Umaru Yar'Adua ya gaji Obasanjo

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Umaru Musa Yar'adua na jam'iyyar PDP, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 21 ga watan Afirilun 2007, inda ya samu ƙuri'u 24,638,063.

Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), ya zo na biyu inda ya samu ƙuri'u 6,605,299, yayin da Atiku Abubakar na jam'iyyar Action Congress (AC) ya samu ƙuri'u 2,637,84.

Zaɓen shugaban ƙasa na 2011: Goodluck Jonathan ya samu nasara

Dr Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2011 da ƙuri'u 22,495,187 inda ya yi nasara akan Muhammadu Buhari na jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), wanda ya samu ƙuri'u 12,214,853.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Yi Kira Mai Daukar Hankali Ga Atiku Da Peter Obi a Jawabin Bankwana

Goodluck Jonathan ya samu nasara a jihohi 23 waɗanda suka haɗa da, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, FCT, Imo, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, da Rivers.

Zaɓen shugaban ƙasa na 2015: Yadda Buhari ya samu nasara

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), ya zama ɗan takarar jam'iyyar adawa na farko da ya kayar da shugaban ƙasa mai ci a shekarar 2015.

Buhari ya lashe zaɓen da ƙuri'u 15,424,921, yayin da shugaba Jonathan na jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 12,853,162.

Zaɓen shugaban ƙasa na 2019: Shugaba Buhari ya yi tazarce

Buhari ya samu ƙuri'u mafi yawa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019, inda ya samu ƙuri'u 15,191,847. Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya zo na biyu da ƙuri'u 11,262,978.

Shugaba Buhari ya samu nasara a jihohi 19 yayin da Atiku Abubakar ya samu nasara a jihohi 18.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Zai Gabatar Da Jawabin Bankwana Ga 'Yan Najeriya, An Bayyana Rana Da Lokaci

Zaɓen shugaban ƙasa na 2023: Bola Tinubu ya samu nasara

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta sanar da Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Bola Tinubu ya samu ƙuri'u 8,794,726 inda ya yi nasara akan Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Peter Obi na jam'iyyar Labour Party sanata Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP).

Lokuta 9 da Aka Rantsar da Shugabannin Kasa a Tarihin Najeriya

A baya rahoto ya zo kan adadin lokutan da aka rantsar da shugabannin ƙasa a tarihin Najeriya.

Ana rantsar da shugabannin ƙasa ne bayan an gudanar da zaɓe a ƙas

Asali: Legit.ng

Online view pixel