Wata Sabuwa: Majalisar Amurka Ta Bukaci Trump Ya Dakata da Yaki da Iran

Wata Sabuwa: Majalisar Amurka Ta Bukaci Trump Ya Dakata da Yaki da Iran

  • Majalisar Wakilan Amurka ta sake kada kuri’ar neman takaita ikon Shugaba Donald Trump na ci gaba da daukar matakin soji kan Iran ba tare da amincewar Majalisa ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa kuri’ar ta samu goyon bayan ‘yan jam'iyyar Trump ta Republican su 7, inda aka kada kuri’u 220 a ranar Talata
  • Wannan shi ne karo na 3 da Majalisar Wakilan Amurka ta amince da irin wannan kudiri tun bayan fara yakin da Iran, yayin da har yanzu ake takaddama a Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri’a kan wani kudiri da zai bukaci Shugaba Donald Trump ya janye sojojin Amurka daga arangama da Iran, sai dai idan Majalisa ta amince da ci gaba da aikin sojin.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta kunyata Shugaban Amurka bayan ya yi maganar komawa teburin sulhu

Rahotanni sun cewa kudirin ya samu kuri’u 220 na amincewa yayin da kuri’u 204 suka nuna adawa da shi. ‘Yan Republican 7 ne suka hada kai da ‘yan Democrat wajen amincewa da kudirin.

Shugaba Donald Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matsayar 'yan majalisar Amurka

CBS ta wallafa cewa kuri’ar ta samu karin goyon bayan ‘yan Republican fiye da kokarin baya na watan Yuni da Yuli na takaita ikon Trump kan yakin Iran.

‘Yan Republican 3 da suka kada kuri’ar amincewa a wannan karon su ne Nancy Mace ta South Carolina, Mariannette Miller-Meeks da Zach Nunn na Iowa.

Sun hade da Tom Barrett na Michigan, Brian Fitzpatrick na Pennsylvania, Warren Davidson na Ohio da Thomas Massie na Kentucky, wadanda suka taba goyon bayan irin wadannan kudurori a baya.

Me ake so Trump ya yi?

Kudirin, wanda dan Democrat Seth Moulton daga Massachusetts ya gabatar, ya bukaci shugaban kasar ya “janye dakarun Amurka daga arangama da Iran.”

Har yanzu ba a tabbatar da ko Majalisar Dattawa za ta duba kudirin ba, musamman ganin cewa sauran mako 2 ne suka rage mata na zaman majalisa kafin zaben watan Nuwamba.

Majalisar kasar Amurka
'Yan majalisar Amurka na tattaunawa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani kudirin makamancin wannan da Majalisar Wakilan ta amince da shi a watan Yuli bai samu wani ci gaba a Majalisar Dattawa ba.

Kara karanta wannan

'Kashe kashe ya yi yawa': An taso gwamna a gaba sai ya bar kujerarsa

Trump ya kare kan shi

Shugaba Trump ya ci gaba da kare dabarar da gwamnatinsa ke amfani da ita kan Iran, yana mai cewa yakin ya rage karfin sojin kasar.

Rahoton Time Magazine ya nuna cewa ya kuma yi hasashen cewa yakin zai kawo karshe nan da nan bayan zaben da za a gudanar.

A yayin muhawarar kudirin, dan Democrat Gregory Meeks daga New York ya ce gwamnatin Trump har yanzu ba ta nuna cewa wata 7 na yakin sun haifar da wata mafita mai dorewa kan barazanar da Iran ke haifarwa ba.

An kai hari Makkah

A wani labari, mun ruwaito cewa kawancen da Saudiyya ke jagoranta wajen yakar kungiyar Houthi a Yemen ya zargi kungiyar da kai hari kan birnin Makka.

Fadan da ake yi tsakanin Houthis da gwamnatin Yemen mai samun goyon bayan Saudiyya ya kuma jawo Riyadh cikin rikicin, yayin da Houthi suka bayyana cewa sun kafa katanga kan zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa Saudiyya.

A wani hari da 'yan Houthi suka kai a baya, kungiyar ta yi ikirarin karbe iko da gabar tekun Yemen da ke Bahar Maliya da kuma mashigar Bab al-Mandab.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng