Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Nade-Naden Mukamai 7 Ana Tsakiyar Rantsar da Tinubu

Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Nade-Naden Mukamai 7 Ana Tsakiyar Rantsar da Tinubu

  • Kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis, ya nada sababbin Darektoci a tashar talabijin na NTA
  • Garba Shehu ya fitar da jawabi da ya tabbatar da haka, amma sanarwar ta zo a kurarren lokaci
  • A yayin da aka sanar da 'yan jarida nadin da aka yi a makon jiya, har Bola Tinubu ya karbi mulki

Abuja - Mai magana da yawun bakin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya sanar da wasu mukamai a makare a makon nan.

Daily Nigerian ta ce sanarwar ta shiga hannun ‘yan jarida a kurarren lokaci, da kimanin karfe 11:00 na safe, lokacin da ana rantsar da sabon shugaban kasa.

Yayin da sanarwar ta fito a safiyar Litinin, Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tun a ranar Juma’a da ta wuce ya yi nadin mukaman nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babban Jigon PDP Kuma Shugaban AIT Ya Mutu Ranar da Tinubu Ya Hau Gadon Mulki

Bola Tinubu
Sabon shugaban kasa, Bola Tinubu Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

Mutum bakwai da aka nada za su zama manyan Darektoci a gidan talabijin NTA.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Garba Shehu

A jawabin da Garba Shehu ya fitar, ya ce a ranar 26 ga watan Mayu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sababbin Darektoci a NTA.

Hakan ya zama dole ne bayan wadanda suke rike da wadannan mukamai a baya sun bar ofis a sakamakon wa’adinsu da ya cika a karshen watan Maris.

Ga sababbin Darektocin da aka nada da kuma jihohinsu:

1. Ije Osagie (Edo) Babban Darektan sashen Injiniyanci

2. Betsy Iheabunike (Anambra) Darektan sashen Kasuwanci

3. Lawal Umar Lalu (Katsina) Darektan sashen Shirye-shirye

4. Ayo Adewuyi (Osun) Darektan sashen Labarai

5. Adamu Sambo (Adamawa) Darektan sashen Harkoki na musamman

6. Nansel Nimyel (Filato) Darektan sashen Gudanarwa da horaswa

7. Abdullahi Ismail Ahmed (Kaduna) Darektan sashen Kudi.

Wa'adi zai kare a shekara uku

Kara karanta wannan

Shagari Zuwa Buhari: Lokuta 9 da Aka Rantsar da Shugabannin Kasa a Tarihin Najeriya

Rahoton ya ce wadanda za su dare wannan kujera za su yi shekaru uku a kai, wa’adin Darektocin tashar kasar zai kare a ranar 26 ga watan Mayun 2026.

Akwai yiwuwar Darekta ya zarce a kujerar na karin shekaru uku, hakan zai bada dama ya sauka a 2029.

Farashin man fetur

Rahoto ya zo cewa kafin Bola Ahmed Tinubu ya gano kujerarsa a Aso Rock, farashin fetur ya fara tashi sama, masu motocin haya sun fara kara kudi tun jiya.

Sabuwar Gwamnati ta ce babu batun tallafin fetur, hakan na nufin ba za a saye litan mai a N200 ba. Farashi musamman a yankin kudancin kasar ya lula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel