Najeriya ta Karrama Mamman Daura, Matar Tinubu, Ganduje da Wasu 340 da Lambar Girma

Najeriya ta Karrama Mamman Daura, Matar Tinubu, Ganduje da Wasu 340 da Lambar Girma

  • Za a karrama tsohon Sakataren kungiyar renon kasashen Birtaniya, Emeka Anyaoku da lambar GCON
  • Gwamnatin tarayya ta zabi mutane fiye da 300 da su ka yi fice a bangarorinsu, domin a karrama su
  • Jerin ya na kunshe da ‘yan siyasa, ‘yan wasa, masu mulki, Sarakuna, daga ciki har da wadanda sun rasu

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi wasu ‘yan Najeriya 340, ya karrama su da babbar shaidar lambo yabo na girma da ake ba ‘yan kasa.

Rahoton Daily Trust ya nuna Emeka Anyaoku ya samu shaidar GCON yayin da Mamman Daura da Mista Godwin Emefiele za su samu lambar CFR.

Sanarwar bada lambar girman ta fito daga Ma’aikatar ayyuka na musamman. A cikin wadanda aka zaba har da ‘yan wasan fim, mawaka da ‘dan kwallo.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Gayyaci Kwankwaso Kaddamar Da Ayyukan Karshe Da Ya Yi A Kaduna

Buhari
Shugaba Buhari a liyafar karshe Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

Bisi Akande da Olusegun Osoba sun samu CFR kamar yadda aka tuna da Samuel Ndanusa Isaiah da Mohammed Barkindo shekaru bayan rasuwarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

David Adeleke (Davido) ya samu OON a dalilin wakokinsa, haka zalika mai shirya fina-finan nan, Kunle Afolayan, an karrama Victor Osimhen da MFR.

A Sarakuna, an zabi Olalekan Mohood Ishola Balogun; Mohammed Sani Haliru Dantoro Kitoro IV; Mohammed Hamim Nuhu Sanusi da kuma wasunsu.

Pantami, Ganduje, Bello

Legit.ng Hausa ta fahimci a jerin akwai Isa Ali Ibrahim Pantami da Hadi Abubakar Sirika.

Tsofaffin Gwamnoni da Ministoci da Sanatoci 75 za su samu CON, daga ciki akwai Babajide Sanwo-Olu, Abdullahi Ganduje da irinsu Yahaya Bello.

A bangaren Sanatoci akwai Adamu Aleiro, Aliyu Wamakko, Ali Modu Sheriff, Ibrahim Gaidam, Abu Ibrahim, Kabir Garba Marafa da kuma Remi Tinubu.

Hadiman Buhari

Rahoton ya ce jerin na kunshe da Abdulrasheed Bawa da hadiman shugaban kasa irinsu Bayo Omoboriowo, Tolani Alli, Sunday Aghaeze da Tolu Ogunlesi.

Kara karanta wannan

Ma’aikatar Gwamnati Ta Samu Sabon Shugaba Ana Saura Awa 96 Buhari Ya Sauka

An bukaci kowanensu ya aika takardunsu kafin 31 ga watan Mayun nan. A ranar 1 ga watan Yuni ne za su samu lamba da shaida daga gwamnatin tarayya.

Tinubu zai karbi kasa

Alkalin Alkalai Olukayode Ariwoola zai rantsar da zababben shugaban na Najeriya a yau Litinin, nan da kusan awa biyu, Bola Tinubu zai karbi iko da kasa.

Yayin da dukkanin iko zai koma kan Tinubu, ku na da labari mukaman da ake sauraro su ne masu magana da baki da shugaban ma’aikatan fadarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel