Jihar Bauchi
Gwamnan Bauchi ya damu kan yadda 'yan bindiga suka dawo dajin Alkaleri, inda ya nemi sojoji su kawo karshen lamarin. Gwamnan ya yi Allah wadai da kisan 'yan banga.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka mutane a jihar Bauchi. 'Yan bindigan sun kuma yi wa wasu mafarauta kwanton bauna a cikin daji.
Wasu matasa sun kai wa tsohon shugaban karamar hukumar Jama'are, Isa Muhammad Wabi hari inda suka yi ajalinsa, ana zargin abokan dansa suka aikata hakan.
Fitaccen matashin dan siyasa, Musa Azare ya ki karɓar mukamin SSA da gwamnan Bauchi ya ba shi, yana mai cewa zai fi amfani idan ya ci gaba da aikinsa na shari’a.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya amince da nada sababbin masu taimaka masa na musamman a bangarori da dama guda 168 don karfafa shugabanci.
Kungiyar matasan APC daga Bauchi ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin cin zarafin ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar da mataimakin gwamnan jihar ya yi.
Sarakunan Arewa da suka hada da Gombe, Bauchi, da sarkin Daura sun nada Ado Doguwa, MA Abubakar, Anas Adamu Muhammad, Sani A A Haruna sarautar gargajiya.
Fostocin neman takarar shugaban kasa a 2027 na Gwamna Bala sun bayyana a titunan Bauchi, yayin da matasa ke cewa wasu ‘yan siyasa sun dauke su aikin tallata gwamnan.
Ɗan ministan harkokin waje na Najeriya, Adam Tuggar ya karyata jita-jitar cewa mataimakin gwamnan Bauchi ya mare mahaifinsa a jihar kan lamarin siyasa.
Jihar Bauchi
Samu kari