Minista Ya Fadi Yadda Gwamnan Bauchi Ya So Sharara Masa Mari a gaban Kashim

Minista Ya Fadi Yadda Gwamnan Bauchi Ya So Sharara Masa Mari a gaban Kashim

  • Ministan harkokin wajen kasar nan, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya tabbatar da cewa an samu hatsaniya da shi a jihar Bauchi
  • Amma ya karyata cewa an samu sabanin ne da mataimakin gwamna, Auwal Jatau, tare da bayyana cewa da gwamna Bala Muhammad aka fafata
  • Ya nanata cewa gwamnan Bauchi ne ya fara takalo shi, har da zagin mahaifinsa kuma ya yi ikirarin zai gaura masa mari a cikin jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana abin da ya haddasa sabani tsakaninsa da Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

Ya musanta rade-radin cewa hatsaniyar ta faru tsakaninsa da mataimakin gwamnan jihar ne, inda ya tabbatar da cewa sun samu sabani mai zafi a gaban Kashim Shettima.

Bauchi
Tuggar ya fadi yadda gwamnan Bauchi ya yi barazanar marinsa Hoto: Ministry of foreign affairs, Nigeria/Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Asali: Facebook

A hirar da ya yi da BBC Hausa, Tuggar ya ce tun daga cikin motar da suka ke tafiya da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, aka fara samun musayar yawu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Gwamnan Bauchi ya zagi mahaifina,' Tuggar

Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana cewa gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ne ya fara tsoma baki a hirar da ba ta shafe shi ba.

Ambasadan ya ce:

“Mun kasance cikin motar da muke raka mataimakin shugaban kasa, sai ya tambaye ni wata magana, amma Gwamna Bala Mohammed wanda ke zaune kusa da shi ya tsoma baki, duk da cewa ba da shi ake magana ba."

Ministan ya cigaba da cewa Gwamnan ya kai har da zagin mahaifinsa, wanda ya rasu fiye da shekaru 20 da suka gabata.

Tuggar: "Gwamnan Bauchi ya so mari na"

Ambasada Yusuf Tuggar ya kara da cewa, baya ga zaginsa da ya yi, Sanata Bala Muhammad ya yunkuro da niyyar dalla masa mari a cikin jama'a.

Ya ce:

'Bayan haka kuma ya zagi mahaifina, mahaifin nan nawa ya yi sama da shekara 20 da mutuwa, sannan kuma bugu da kari gwamnan ya tashi ya ce zai mare ni, wanda kuma ni na ga in an kyale mu ni ban ga yadda zai iya yi min duka ba ko ya mare ni saboda haka ni ma na tashi na gwada masa tsawo.''
''Bayan haka shi ne mataimakinsa ya sheko a guje daga bayan wannan mota bas, kan cewa shi ma zai zo ya mare ni, amma bai iya ko karasowa ko kusa da ni ba, saboda kar ka manta cewa mataimakin shugaban kasa yana cikin wannan mota."

Ya zargi wasu da ake zaton yaran gwamnan da yada labaran ƙarya a shafukan yanar gizo cewa mataimakin gwamnan, Auwal Jatau, ne ya mare shi

Gwamna
Tuggar ya ce gwamnan Bauchi ya zagi mahaifinsa a Bauchi Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Asali: Facebook
“Wannan ba gaskiya ba ne. Shi kansa Jatau ya san ba a yi hakan ba, daga baya ma suka sauya labari cewa wai ba a mare ni."

Bauchi: Ana son binciken cin zarafin Tuggar

A baya, mun wallafa labarin cewa wata ƙungiyar matasan APC ta nemi a gudanar da bincike kan zargin da ake yi na cin zarafin Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar.

Kungiyar ta bayyana cewa akwai bukatar hukumomin tsaro su binciki abin da ya faru a filin jirgin sama na Bauchi, yayin ziyarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

A cewar wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Musa G. Khalid, ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce abin da ya faru ya saba da duk wata dabi’ar dimokiradiyya, sannan ya ci mutuncin Ministan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.