Yan Bindiga Sun Kai Harin Ta'addanci bayan Samun Labarin Gwamnati Ta Bayar da Tallafin Kudi a Sokoto
- ’Yan bindiga dauke da makamai un kai hari Gorau da ke Goronyo, inda suka kashe mutane huɗu tare da sace wasu huɗu
- Maharan sun harbi mutane 11, inda huɗu suka mutu nan take, yayin da aka garzaya da sauran bakwai asibiti
- Ana zargin ’yan bindigar sun kai harin ne domin neman kuɗin tallafin N1m da gwamnatin Sokoto ta bai wa iyalan waɗanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - ’Yan bindiga sun kashe mutane huɗu tare da yin garkuwa da wasu huɗu a ƙauyen Gorau da ke ƙaramar hukumar Goronyo a Jihar Sokoto.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Laraba, 26 ga watan Agustan 2026 kwanaki shida kacal bayan wani hatsarin kwale-kwale a yankin ya yi sanadin mutuwar mutane 65.

Source: Original
Maharan sun kuma harbe mutane bakwai, waɗanda suka samu raunuka kuma ake kula da su a wani asibiti, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
'Yan bindiga sun rika neman wadanda aka ba tallafi
Rahotanni sun ce maharan sun fi mayar da hankali ne kan iyalan da suka kasance cikin waɗanda gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da ba wa tallafin N1m ga kowannen su.
Shugaban ƙauyen Gorau, Alhaji Aliyu Magaji Na-Batsami, ya tabbatar da harin, inda ya ce ’yan bindigar sun riƙa shiga gidaje ɗaya bayan ɗaya suna neman kuɗin tallafin.
Ya ce maharan sun kutsa kusan kowane ɗaki a gidansa yayin da suke tambayar inda aka ajiye N1m da aka bai wa iyalan waɗanda hatsarin ya shafa.
“Sun harbi mutane 11. Huɗu sun mutu nan take, yayin da aka kai sauran bakwai asibiti domin jinya. Sun kuma yi garkuwa da wasu huɗu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa maharan sun kai harin ne saboda kuɗin tallafin da aka bai wa iyalan waɗanda hatsarin kwale-kwalen baya-bayan nan ya shafa.
An bayyana sunayen waɗanda aka kashe
Shugaban ƙauyen ya bayyana sunayen mutane huɗun da aka kashe a harin da suka haɗa da Bashar Sani, Ila Malam Makeri, Isa Ibrahim da Ali Aminu.
Ya ce yawan waɗanda suka mutu ko suka jikkata zai iya ƙaruwa idan jami’an tsaro ba su gaggauta kai ɗauki ba.
“Muna godiya ga jami’an tsaro saboda gaggawar da suka yi wajen kawo ɗauki. Sun zo da motoci huɗu suka bi bayan ’yan bindigar,” in ji shi.
Harin ya biyo bayan mutuwar mutane 65
Harin ya faru ne ƙasa da mako guda bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da mazauna Gorau ya kife, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 65.
Yawancin waɗanda suka mutu yara ne, musamman mata ‘yan mata, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin jimami.
Bayan wannan mummunan hatsari, gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da tallafin N1m ɗaya ga kowane iyalin waɗanda suka rasa ‘yan uwansu, tare da rabon kayan abinci domin rage musu radadi.
Sai dai sabon harin ya ƙara jefa damuwa kan tsaron iyalan mamatan da kuma yadda za a kare kuɗaɗen tallafin da aka bai wa waɗanda lamarin ya shafa.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun sace dan kasuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani ɗan kasuwa, Alhaji Yusuf Keche.
Maharan sun sace sanannen dan kasuwar ne bayan ya idar da Sallar Isha’i a wani masallaci da ke Dabi, Karamar Hukumar Kwali da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng


