Rigima Ta Kaure Tsakanin Yaron Gwamnan Bauchi da Ɗan Minista kan Zargin Marin Tuggar
- Ɗan ministan harkokin waje na Najeriya, Adam Tuggar ya karyata jita-jitar cewa mataimakin gwamnan Bauchi ya mare mahaifinsa a jihar
- Ya bayyana Shamsuddeen Bala, ɗan gwamnan Bauchi, da mai yaɗa ƙarya da kuma rashin tarbiyya, yana ƙara da cewa bai taɓa shiga siyasa ba
- Adam ya ce da ace an mari mahaifinsa, da an hadawa mai marin jini da majina a hanci, yana kuma cewa Shamsuddeen bai san siyasa ba
- Kakakin mataimakin gwamnan ya musanta zargin, yana cewa Mohammed Jatau ba zai taba marin minista ba saboda halayensa na dattako da mutunci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Ɗan ministan harkokin waje na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yi magana rigima da mahaifinsa a Bauchi.
Adam Tuggar ya karyata rahotannin da ke cewa mataimakin gwamnan Bauchi, Auwal Jatau, ya mari mahaifinsa.

Asali: Twitter
Ɗan Tuggar ya soki yaron gwamnan Bauchi
Hakan na cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook inda ya caccaki dan gwamnan Bauchi, Shamsuddeen Bala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma soke shi yana zarginsa da yaɗa ƙarya da kuma neman ɓata suna inda ya ce bai taɓa shiga muhawarar siyasa ba a intanet.
Tuggar ya ce:
“Wannan abun kunya daga ɗan gwamna mai girman kai da kuma ‘yan jaridunsa yasa dole na yi magana da ƙarfi.
"Gaskiya ban taɓa ganin jahilin da ya yi karatu irin sa ba, yaɗa wannan ƙarya kawai na nuna ba ya canzawa.
"Ba abin mamaki ba ne ganin yadda ya taba zagin manyan mutane irinsu Atiku Abubakar saboda kawai sun saba ra’ayin siyasa da mahaifinsa."

Asali: Facebook
Adam Tuggar ya kalubalanci Shamsu a Bauchi
Adam ya ce abin da Shamsuddeen Bala ya yi da zagin Tuggar ba daidai ba ne kuma yana nuna rashin tarbiyya.
Ya ƙara da cewa:
"Ko da labarin ƙaryar gaskiya ne, da har mahaifinka ne ya mare Tuggar, da ya koma gida da jini a hanci da baki.
“Ina kakanka ya ke a lokacin? Waye shi? Me ya taɓa yi wajen cigaban jihar Bauchi ko ƙasa gaba ɗaya?
“Tuggar kamar sauran masu neman takara bai nuna sha’awar tsayawa ba. To me yasa wannan hayaniya da neman daga hankali?
“Ku maimakon ku duba ayyukan Bauchi, kuna yaɗa labaran ƙarya a kafafen watsa labarai. Ba mamaki ku aikata haka, kai da mahaifinka kun taɓa zama a gidan gyaran hali."
“Yawon satar dukiyar al’umma yana yawo a cikin jininku. Ku sani idan manya na fada, ku rufe baki ku tsira da mutuncinku kaɗan.”
Mataimakin gwamnan Bauchi ya musanta marin minista
Kun ji cewa mataimakin gwamnan Bauchi, Mohammed Auwal Jatau, ya musanta zargin cewa ya mari ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar.
Lamarin da ake cewa ya faru a cikin bas ya haddasa cece-kuce, inda wasu ke cewa rikici ya ɓarke bayan cin fuska ga Gwamna Bala Mohammed.
Mai magana da yawun Jatau ya ce ba a taɓa samun hakan ba a Bauchi, yana ƙalubalantar masu da’awar da su kawo hujjoji.
Asali: Legit.ng