Sojojin Amurka da aka Jibge a Bauchi Sun Fara Aikin da Suka Zo Yi Najeriya

Sojojin Amurka da aka Jibge a Bauchi Sun Fara Aikin da Suka Zo Yi Najeriya

  • Rundunar sojin Amurka ta fara horas da sojojin Najeriya kan amfani da jirage marasa matuka da sauran dabarun aikin soja a jihar Bauchi
  • Horarwar ta kuma shafi kula da sojojin da suka samu raunuka a fagen daga, a wani yunkuri na kara karfafa hadin gwiwar tsaro
  • Amurka ta ce an tsara horarwar ne bisa bangarorin da rundunar sojin Najeriya ta zaba domin inganta kwarewar jami'anta da kuma kara karfin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – Rundunar sojin Amurka ta fara horas da sojojin Najeriya kan amfani da jirage marasa matuka, kula da wadanda suka samu raunuka a fagen daga da sauran dabarun aikin soja.

An gudanar da horarwar ne a jihar Bauchi a matsayin wani bangare na yunkurin kara karfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari fadar sarki, an tarwatse ana tsaka da bikin gargajiya

Sojojin Amurka da sojojin Najeriya
Sojojin Amurka na ba na Najeriya horo. Hoto: @USAfricaCommand
Source: Twitter

Rundunar sojin Amurka ta wallafa a X cewa an bai wa shugabannin sojojin Najeriya zabin bangarori daban-daban na horo, inda suka zabi wadanda suka ga za su fi amfani wajen inganta ayyukan rundunarsu.

Amurka na horas da sojin Najeriya

Jami'in kula da kayan aiki na rundunar sojin Amurka a Afrika, Kyaftin Gabriel Feingold, ya ce horarwar ta gudana ne bisa bukatun rundunar sojin Najeriya.

Ya ce ana gabatar wa sojojin Najeriya batutuwa daban-daban na horo domin su zabi bangarorin da suka fi dacewa da bukatunsu.

Rundunar AFRICOM ta ce sojojin Najeriya sun nuna matukar sha'awar koyon yadda ake amfani da jirage marasa matuka wajen ayyukan soja.

Wani masani kan harkokin tattara bayanan sirri, Sajan Mark Murphy ya horar da kusan mambobi 10 na rundunar sojojin saman Najeriya.

Sojojin Amurka a Najeriya
Wasu sojojin Amurka da Bola Tinubu a Aso Rock Villa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Channeles TV ta rahoto cewa horarwar ta fara da kusan mintuna 45 na koyarwa a aji, kafin daga bisani mahalartan su shiga aikin gwaji da amfani da jiragen marasa matuka.

Kara karanta wannan

An 'gano' lokacin da sakataren rundunar sojin Amurka zai yi murabus

Murphy ya kuma koyar da sojojin yadda za su tura jiragen da kuma amfani da bayanan sirrin da aka samu ta hanyarsu wajen gudanar da ayyukan soja.

Batun alakar Najeriya da Amurka

Baya ga koyar da dabarun fasaha da na aikin soja, rundunar AFRICOM ta ce atisayen hadin gwiwar na da nufin kara dankon zumunci da fahimtar juna tsakanin sojojin kasashen biyu.

Feingold ya ce irin wannan hadin gwiwa na taimakawa wajen gina kyakkyawar alaka tsakanin sojojin Amurka da na Najeriya.

Ya kara da cewa hakan na taimakawa bangarorin biyu wajen fahimtar yadda za su yi aiki tare da kuma musayar kwarewa.

Iran na neman dan Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa gidan talabijin na gwamnatin Iran ya watsa wani rahoto da ya nuna yunkurin gano hanyar isa ga dan shugaban Amurka, Barron Trump.

Rahoton ya kuma ambaci batun kyautar dala miliyan 10, inda aka bayyana hanyoyin da ake kokarin gano wuraren da Barron Trump yake da kuma mutanen da ke kusa da shi.

An nuna wasu hotuna masu kama da bayanan sa ido, tare da bayanai kan yunkurin gano hanyoyin da za a iya bi domin kutsawa cikin tsauraran matakan tsaron Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng