Yadda 'Yan China Suka Shirya Kutsen Intanet a Ma'aikatun Amurka
- Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce ta dakile wasu abubuwan kutse guda biyu, QScan da QTRouter, da aka yi amfani da su wajen kutse cikin na’urorin da ke haɗe da intanet
- An yi amfani da waɗannan abubuwan ne wajen kai hare-hare kan muhimman cibiyoyin Amurka, ciki har da NASA da Majalisar Dattawan Amurka
- Hukumar ta ce wani kamfanin China mai suna Nanjing Xinjiuwei ne ke lura da abubuwan, kuma ana zargin hukumomin leƙen asiri da sojojin China na amfani da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Amurka ta ƙaddamar da wani samame na musamman da ya kai ga rufe wasu dandalolin kutse na yanar gizo da ake zargin wani kamfanin China ke sarrafa su.
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta sanar da matakin a ranar Laraba, inda ta ce an ƙwace QScan da QTRouter, waɗanda aka yi amfani da su wajen kutsawa cikin na’urorin da ke haɗe da intanet tare da ɓoye ainihin inda hare-haren ke fitowa.

Source: Getty Images
Wadanda suka yi kutse a Amurka
Al Jazeera ta ce a cewar takardun kotu, an yi amfani da kayayyakin fasahar wajen lalata ko kutsawa cikin muhimman hanyoyin sadarwa da wasu cibiyoyi masu muhimmanci a Amurka da sauran ƙasashe tun aƙalla shekarar 2018.
Masu kutse sun yi ƙoƙarin shiga hanyoyin sadarwar NASA a watan Agustan 2019, sai dai ba su yi nasara ba.
Sai kuma a watan Satumban 2024, suka yi nasarar kutsawa cikin hanyoyin sadarwar wasu dakunan gwaje-gwaje uku na Ma’aikatar Makamashi ta Amurka, da NIH, HHS da kuma wani kamfanin kera na’urorin tsaro na Amurka.
Majalisar Dattawan Amurka da wasu kamfanoni huɗu da ba a bayyana sunayensu ba a Amurka da Koriya ta Kudu, na daga cikin waɗanda aka bayyana cewa an kai wa hari.
China na da hannu a harkar?
Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta ce wani kamfanin China mai suna Nanjing Xinjiuwei Network ne ke gudanar da dandalolin kusten.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yadda yan bindiga suka rika tashin mutane daga barci, su harbe su har lahira
Ta kuma zargi kamfanin da samar da ayyukansa ga wasu hukumomin China, ciki har da Ma’aikatar Tsaron Ƙasa da kuma rundunar sojin ƙasar.
Ta ce QScan na taimaka wa masu kutse wajen gano dubban na’urorin da ke haɗe da intanet, ciki har da na'urorin sadarwa, sannan a shigar da su cikin wata babbar hanyar sadarwa ta amfani da QTRouter.

Source: Getty Images
Wannan tsarin ya ba masu kutse damar karkatar da hare-harensu ta cikin kwamfutoci da wasu na'urori da ke wajen China, ta yadda harin da aka kai wa wani wuri a Amurka zai iya bayyana kamar ya fito ne daga wata na’ura da ke wani ƙasa.
Rasha za ta gana da Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran da Rasha na shirin ƙara zurfafa haɗin gwiwarsu a fannin makamashin nukiliya, yayin da ake sa ran Masoud Pezeshkian da Vladimir Putin za su gana a Kyrgyzstan.
Ganawar shugabannin biyu za ta gudana ne a yayin taron SCO da za a yi a Bishkek, kamar yadda Jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya bayyana.
Jalali ya ce Iran da Rasha sun kuma amince da yarjejeniyar fahimtar juna ta dala biliyan 25 domin gina sabbin tashoshin makamashin nukiliya.
Asali: Legit.ng
