Ranar Hausa: Sarkin Musulmi Ya ba Hausawa, Fulani Shawara da Alaka ke Neman Baci
- Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga Hausawa da Fulani kan aminci a tsakaninsu
- Sultan ya ce al’ummomin biyu suna da tarihi, al’adu da addini iri ɗaya, don haka bai kamata su bari wasu abubuwa su raba su ba
- Ya yi wannan kira ne a taron Ranar Hausa ta Duniya karo na 12 da aka gudanar a Sokoto, inda aka jaddada muhimmancin haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga Hausawa da Fulani da su kawo ƙarshen rashin yarda da ke tsakaninsu.
Ya ce ya kamata al’ummomin biyu su ƙara kusantar juna, su kuma ƙarfafa fahimtar juna domin samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Source: Facebook
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 12 da aka gudanar a Sokoto, cewar The Nation.
Shawarar Sarkin Musulmi ga Hausawa, Fulani
Sultan ya kuma bukace su da kada su bari a raba su, yana mai cewa ya kamata su haɗa kai domin zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Junaid, ne ya wakilci Sultan a wajen taron da reshen Sokoto na Hausa/Fulani Youth Development and Orientation Forum, HAFYDOF, ya shirya.
Ya ce yana da matuƙar muhimmanci Hausawa da Fulani, waɗanda ke da alaƙar al’adu da addini, su haɗa kai domin tabbatar da dorewar haɗin kansu.
Sultan ya danganta tarihin alaƙar Hausawa da Fulani da Sheikh Usmanu bn Fodiyo, wanda ya taimaka wajen gina tushen haɗin kai tsakanin al’ummomin biyu.
Ya ce wannan haɗin kai ya ƙarfafa dangantakar addini, kasuwanci da auratayya tsakanin Hausawa da Fulani tsawon shekaru masu yawa.
Ya jaddada cewa:
“Dole ne mu haɗa kai domin zaman lafiya da haɗin kan ƙasar nan.”

Source: Facebook
An bukaci Fulani, Hausawa su gyara alaka

Kara karanta wannan
Maulidin Annabi SAW: Yaran Matawalle sun ba Musulmi shawara ana shirin zaben 2027
A jawabinsa na buɗe taron, Sa’in Kilgori Muhammad Kilgori ya ce Hausawa da Fulani sun shafe shekaru da dama suna da amana da fahimtar juna.
Ya bayyana cewa al’ummomin biyu suna da kamanceceniya mai yawa a fannin al’adu da al’adun gargajiya, wanda bai kamata a bari ya ɓace ba, cewar Punch.
Kilgori ya ce bikin Ranar Hausa wata muhimmiyar dama ce ta nuna muhimmancin harshen Hausa da kuma dangantakarsa da Fulani da salon rayuwarsu.
Ya ce:
“Dole ne mu guji zarge-zarge da munanan farfaganda da suka raba mu, mu yi amfani da amana ta dogon lokaci wajen gina ƙasa mai zaman lafiya da haɗin kai.”
Shugaban gundumar Kilgori ya kuma bayyana cewa Hausawa da Fulani sun daɗe suna rayuwa cikin zaman lafiya, tare da yin auratayya ba tare da wani shinge ba.
Ya yi baƙin ciki kan yadda rashin yarda ya fara bayyana tsakanin al’ummomin biyu, yana mai cewa irin wannan taro zai taimaka wajen sake gina amana.
Tinubu ya yaba wa tasirin Hausawa
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana Hausawa a matsayin manyan ginshikai da ke taka muhimmiyar rawa wajen hadin kai da ci gaban Najeriya.
Tinubu ya ce harshen Hausa ya bunkasa sosai, inda ya zama daya daga cikin manyan harsunan hadin kai da kasuwanci a duniya.
Shugaban kasar ya taya al'ummar Hausawa murnar Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 26 ga watan Agustan 2026.
Asali: Legit.ng

