Amurka Ta Fadi Abin da Ta ke Koya wa Sojojin Najeriya a Jihar Bauchi
- Sojojin Amurka da Najeriya sun gudanar da jerin atisayen soji a Bauchi domin musayar ƙwarewa da ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu
- Atisayen ya ƙunshi koyar da dabarun kula da sojojin da suka jikkata, amfani da makamai, da wasu dabaru da suka shafi abubuwa masu fashewa
- Jami’an Amurka sun ce atisayen na taimaka wa wajen ƙulla kyakkyawar alaƙa da takwarorinsu na Najeriya, musamman a matakin ƙananan rundunoni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Sojojin Amurka da Najeriya sun gudanar da jerin atisayen soji a jihar Bauchi, a wani mataki na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro, musayar ƙwarewa da inganta dabarun gudanar da ayyukan soji tsakanin ƙasashen biyu.
Sajan Mark Murphy, jami’in nazarin bayanan leƙen asiri da ke aiki da bataliyar yaƙi ta 13 ta sojojin Amurka, ya ce horar da sojoji na daga cikin muhimman ayyukan da yake jin daɗin gudanarwa.

Source: Facebook
Wannan nankunshe a cikin sakon da bangaren rundunar sojin Amurka da ke kula da yankin Afrika ya wallafa a shafin ta na X a ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, 2026.
Ana hada gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya
A cewar jami’an Amurka, shirin haɗin gwiwar tsaro da ake gudanarwa a Bauchi na da nufin ƙarfafa shirye-shiryen yaƙi, inganta ƙwarewar sojoji da kuma samar da kyakkyawar alaƙa mai ɗorewa tsakanin rundunonin ƙasashen biyu.
Sajan Mark Murphy ya ce:
“Ina son horar da sojoji. Ina ganin horar da sojoji da shirya su domin aiki na daga cikin manyan ayyukan rundunar NCO a cikin sojoji."
Ta hanyar atisayen haɗin gwiwa, ba da shawarwari, musayar bayanan leƙen asiri da kuma musayar ƙwarewar ƙwararru, sojojin ƙasashen biyu na ƙoƙarin inganta iya aiki tare wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka shafi ƙasashen biyu.
Abubuwan da sojin Najeriya ke koya
Atisayen na Bauchi ya haɗa da koyar da dabarun ceton rayukan sojoji a fagen daga, kula da waɗanda suka samu munanan raunuka, da sanin makamai da yadda ake amfani da su.

Source: Original
Sai kuma dabarun ɓoye sojoji, sarrafa da gwajin ruwa, kwance abubuwan fashewa, dabarun ƙananan rundunoni da kuma amfani da jiragen sama marasa matuƙi.
Kyaftin Gabriel Feingold, jami’in kula da kayan aiki na Rundunar Sojin Amurka ta Kudancin Turai da Afrika, wanda kuma ke kula da ayyuka a Wurin Gudanar da Ayyukan Bauchi, ya ce sun gano abubuwan da ya fi dacewa a koyar.
Ya ce wannan tsarin na ba da damar amfani da ƙwarewar jami’an Amurka da ke Bauchi tare da mayar da hankali kan abubuwan da sojojin Najeriya suka fi buƙata.
Yan bindiga sun shammaci jami'an tsaro
A baya, an ji cewa an bindiga sun kashe jami’an tsaro biyu a harin da suka kai Tanjol da Tarai a gundumar Jol, Riyom, jihar Plateau da ta dade tana fama da rikice-rikice.
Maharan sun kwace bindigun jami’an da aka kashe, yayin da wasu mutane suka jikkata kuma aka rawaito cewa wani farar hula ya bace a yayin da ake ci gaba da musayar wuta.
Harin ya ƙara tayar da fargaba a Riyom, inda aka samu wasu hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro a makonnin baya a yankin da ke ama da rikice-rikice masu tayar da hankali.
Asali: Legit.ng

