Sarakunan Arewa Sun Ba Manyan Mutane Sarauta a Katsina da Wasu Jihohi
Daga kammala sallar azumin shekarar 2025, sarakunan Arewa sun nada 'yan siyasa da 'yan kasuwa sarauta a jihohin Kastina, Gombe da sauransu.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Tun bayan kammala bikin sallar azumin shekarar 2025 wasu sarakunan Arewa suka fara nada 'yan siyasa da wasu 'yan kasuwa sarauta.
'Dan majalisar wakilai daga Kano, Alhassan Ado Doguwa da tsohon gwamnan jihar Bauchi, MA Abubakar na cikin wadanda aka ba sarauta a jihohi.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu manyan mutanen da sarakunan Arewa suka ba sarautar gargajiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Alhassan Ado Doguwa
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya nada Hon. Alhasan Ado Doguwa a matsayin Sardaunan Ƙasar Hausa Mai Tuta.

Asali: Facebook
An gudanar da bikin nadin sarautar gargajiya ga ɗan majalisar tarayya, Hon. Alhasan Ado Doguwa, mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun ne a Daura.
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ne ya jagoranci nadin sarautar, inda ya ba shi sarautar Sardaunan Ƙasar Hausa Mai Tuta a wani biki mai armashi.
Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook cewa Taron ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban.

Asali: Facebook
Daga cikin manyan baki da suka halarci bikin akwai Sanata Muntari Dandutse daga Katsina ta Kudu.
Hakazalika, Sanata Ibrahim Lamido daga Sokoto ta Gabas, shugaban kwamitin lafiya da cututtuka masu kamari a majalisar Dattawa, ya kasance cikin wadanda suka shaida bikin.
Sun yi godiya ga Sarkin Daura bisa girmamawan da yi waa Ado Doguwa, tare da yaba masa bisa jajircewarsa a fagen siyasa da hidimar al’umma.
Baya ga Hon. Doguwa, an kuma nada wasu mutane biyu da suka yi fice a cikin al’umma a matsayin masu rike da sarautun gargajiya.
Hon. Hamza Usman Faskari ya samu nadin sarautar Sadaukin Ƙasar Hausa, yayin da Sagir Bala ya zama Bulaman Ƙasar Hausa.
2. Tsohon gwamnan Bauchi, MA Abubakar
Birnin Bauchi ya cika da baki daga sassa daban-daban na kasar nan yayin da aka gudanar da nadin sarauta ga tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar.
Rahotanni sun nuna cewa an yi bikin nada Mohammed Abubakar a matsayin Makama Babba na masarautar Bauchi.

Asali: Facebook
Taron ya kuma kunshi daurin auren diyarsa, Khadija Mohammed, wanda aka yi a fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Suleiman Adamu.
Bikin ya ja hankalin fitattun mutane ciki har da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban gwamnonin Arewa, gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Haka zalika, ministoci, ‘yan majalisa da manyan ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban na kasar nan sun halarci bikin domin nuna goyon baya da girmamawa ga tsohon gwamnan.
3. Alhaji Anas Adamu Muhammed
A wani gagarumin biki da aka gudanar a jihar Gombe, mai martaba Sarkin Gombe (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar III CFR ya nada Alhaji Anas Adamu Mohammed Dokajin Gombe.
Bikin dai ya gudana da yammacin ranar Asabar, 19 ga Afrilu, 2025, inda wakilan da sarkin Gombe ya tura suka jagoranci tabbatar da wannan sarauta mai daraja a gidan Arc. Yunusa Yakubu.
Taron ya samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen jihar Gombe, da kuma masu rike da mukamai na gargajiya da na gwamnati.

Asali: Facebook
Wakilan da Sarkin Gombe ya tura sun haɗa da Shamakin Gombe, Alh. Usman Mohammed, wanda ya jagoranci tawagar.
Sauran wadanda suka halarci bikin sun sun hada da Salaman Gombe Alhaji Usman Adamu Barde, Shettiman Gombe Usman Shettima, Mabudin Gombe Alhaji Umaru Abdullahi Babagoro.
Sauran sun hada da Libidin Gombe Sadiq Libidi da kuma Idayan Gombe Alh. Abdullahi Bappah Idaya, wadanda duk sun wakilci fadar sarkin wajen tabbatar da sarautar Dokajin Gombe.
Alhaji Anas shahararren dam kasuwa ne da ya yi fice wajen yin gine gine a fadin Najeriya, kuma shi ne shugaban kamfanin gini na Salbrix kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Hadimin gwamnan jihar Gombe, Abdul No Shaking ne ya wallafa yadda taron sarautar ya gudana a shafin shi na Facebook.
4. Hon. Sani Ahmad Haruna
Mai martaba sarkin Gombe ya nada shugaban karamar hukumar Gombe, Hon. Sani Ahmad Haruna Wakilin Arewan Gombe.
Bayan samun nadin sarautar, shugaban majalisar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar Gombe, Hon. Sani Ahmad Haruna Esq, ya kai ziyarar gaisuwar godiya ga fadar sarkin Gombe.
Ziyarar ta gudana ne domin nuna godiya bisa sa masa rigar mutumci da Sarkin Gombe, Alhaji (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar III CFR, ya yi ta hanyar ba shi sarautar Wakilin Arewan Gombe.
Taron wanda ya gudana cikin girmamawa da tarin manyan baki, ya zama wata dama ta sake bayyana haɗin kai tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya a jihar Gombe.

Asali: Facebook
Abdul No Shaking ya wallafa a Facebook cewa Hon. Haruna, ya samu rakiyar fitattun shugabannin ƙananan hukumomi, tare da kwamishinoni, kansiloli da jami’an gwamnati.
Buba Galadima ya yi magana kan Sarki Sanusi II
A wani rahoton, kun ji cewa jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya ce duk abin da ake kullawa sarki Muhammadu Sanusi II ba zai yi nasara ba.
Buba Galadima ya ce ko da za a sauke Muhammadu Sanusi II daga sarauta sau 10 to za su mayar da shi.
'Dan siyasar ya yi magana ne yayin da ake cigaba da takaddama kan sarautar Kano, musamman a bangaren Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng