An Hallaka Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Bauchi, Ana Zargin Abokan Ɗansa

An Hallaka Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Bauchi, Ana Zargin Abokan Ɗansa

  • Tsohon shugaban karamar hukumar Jama'are, Isa Muhammad Wabi, ya mutu bayan abokan dansa sun kai masa hari da asuba a Bauchi
  • ‘Yan sanda sun ce an samu kiran gaggawa daga wani mutumin kirki da ya bayyana harin da wasu matasa suka kai a Fadaman Mada
  • Bincike ya nuna cewa Ahmad Abdulkadir (Abba) da Faruk Malami (Ajebo) ne suka shiga gidan da karfe 3:00 na dare suka kai masa farmaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Tsohon shugaban karamar hukumar Jama’are a jihar Bauchi, Isa Muhammad Wabi, ya mutu sakamakon wani harin da aka kai da safe a gidansa.

An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Juma'a 1 ga watan Mayun 2025.

An cafke wani da zargin kisan tsohon shugaban karamar hukuma
Ana zargin kisan tsohon shugaban karamar hukuma kan abokan ɗansa a Bauchi. Hoto: Legit.
Asali: Original

An hallaka tsohon shugaban karamar hukuma

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da kakakinta, Ahmed Wakil, ya fitar a ranar Juma’a da aka wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakil ya ce:

"Da safiyar Juma’a, 2 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 04:03 na safe, rundunarmu ta samu kiran gaggawa daga wani mutumin kirki.
“Kiran ya shafi wani hari da wasu matasa suka kai a Fadaman Mada, da ke bayan makarantar sakandare ta ‘yan mata a Bauchi.
“Nan da nan jami’an rundunar suka isa wurin. Sun tarar da Isa Muhammad Wabi, mai shekara 66, cikin mawuyacin hali da raunuka masu tsanani.
“An garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi domin samun kulawar gaggawa."
An cafke wani da zargin kisan tsohon shugaban karamar hukuma
Yan sanda sun kama wani da zargin hannu a hallaka tsohon shugaban karamar hukuma a Bauchi. Hoto: Bauchi State Police Command.
Asali: Facebook

Ana binciken kiwan tsohon shugaban karamar hukuma

Wakil ya ce bincike na farko ya nuna cewa wadanda suka kai harin abokan dansa Abdulgafar Isa Mohammed ne, wanda yake da shekaru 24.

Ya ce:

“Bincike ya nuna cewa Ahmad Abdulkadir wanda aka fi sani da Abba, da Faruk Malami (Ajebo), sun shiga gidan da misalin karfe 03:00.
“Sun shirya kai masa hari, inda suka daba masa wuka sau da dama a wuyansa. An kai shi asibiti, daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.”

Kakakin yan sanda ya ce daya daga cikin wadanda ake zargi, wato Ajebo, an same shi a sume a wurin da lamarin ya faru.

Sanarwar ta ce an kama Abdulgafar Isa Mohammed domin gudanar da tambayoyi, kuma yana bayar da hadin kai da bayanai masu amfani.

Wakil ya ce rundunar tana gudanar da cikakken bincike domin gano yadda lamarin ya faru da kuma hukunta duk masu hannu.

Dattijo ya dirkawa ƴarsa ciki a Bauchi

A baya, kun ji cewa wani dattijo dan shekaru 50, Umar Sule, ya shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin dirka wa ’yarsa mai shekaru 17 ciki a jihar Bauchi.

Lamarin ya faru ne a Kurmin Ado, karamar hukumar Ganjuwa, inda wanda ake zargi ya amsa cewa ya yi lalata da 'yarsa babu adadi.

Jami’an tsaro na ci gaba da bincike yayin da kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.