Siyasa Ta Dauki Zafi, Bola Tinubu Ya Shiga Ganawa da Gwamnonin APC a Aso Rock

Siyasa Ta Dauki Zafi, Bola Tinubu Ya Shiga Ganawa da Gwamnonin APC a Aso Rock

  • Shugaban Najeriya, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
  • Taron ya fara ne jim kaɗan kafin ƙarfe 4:00 na yammacin Alhamis, 27 ga watan Agustan 2027 amma har kawo yanzu babu cikakken bayani
  • Ganawar ta zo ne kwanaki takwas bayan fara yaƙin neman zaɓe a hukumance bisa jadawalin hukumar INECBgabanin zaɓen 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya shiga ganawa yanzu haka da gwamnonin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Taron, wanda ya haɗa da mambobin kungiyar gwamnonin APC (PGF), ya fara ne jim kaɗan kafin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2027.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ganawar ta zo ne bayan wani zama na daban na Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC) wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Tirkashi: APC ta dauka da zafi bayan Atiku ya yi wasu kalamai

Dalilin ganawar Tinubu da gwamnonin APC

A lokacin hada wannan rahoto, taron na Tinubu da gwamnonin APC yana ci gaba da gudana, yayin da ba a bayyana cikakkun bayanai kan ajandar taron ba.

Ganawar ta Tinubu da gwamnonin APC ta zo ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

An gudanar da taron ne kwanaki takwas bayan fara yaƙin neman zaɓe a hukumance, bisa jadawalin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar.

APC ta kafa kwamitin kamfen 2027

Haka kuma, ganawar ta zo ne kwanaki biyar bayan jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishinan INEC ya saka Atiku da Tinubu a sikeli, ya fadi wanda zai lashe zaɓen 2027

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ne aka naɗa Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen.

Me ake tattaunawa a wurin taron?

Ana sa ran ganawar Tinubu da gwamnonin APC za ta samar da damar tattaunawa kan haɗin kai a harkokin siyasa, tattara magoya baya da sauran batutuwan da suka shafi jam’iyya mai mulki gabanin zaɓen 2027.

Gwamnonin APC.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnonin APC a Aso Rock Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Kungiyar gwamnonin APC ta PGF ta kasance muhimmin dandamali wajen haɗa kai da daidaita ayyuka tsakanin gwamnonin APC, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

An kuma sa ran Shugaba Tinubu ya ci gaba da ganawa da shugabannin jam’iyyar da zaɓaɓɓun jami’anta yayin da APC ke ƙara shirye-shiryenta domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Gwamnoni sun yi maganar kudin tallafin mai

A wani labarin, kun ji cewa gwamnoni sun yi watsi da zargin cewa gwamnatocin jihohi sun kasa yin bayani kan yadda suka kashe kuɗin da aka samu bayan cire tallafin mai.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana hakan ta bakin gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, bayan taron da suka gudanar a Abuja.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce tana duba wani sabon shiri na amfani da motocin CNG domin rage kuɗin sufuri da sauƙaƙa wa talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262