Bauchi: Ana Jita Jitar Zai Nemi Shugabancin Najeriya, Gwamna Ya Naɗa Hadimai 168

Bauchi: Ana Jita Jitar Zai Nemi Shugabancin Najeriya, Gwamna Ya Naɗa Hadimai 168

  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed na jihar Bauchi ya amince da nada sababbin masu taimaka masa guda 168 don karfafa shugabanci
  • Hadiminsa, Mukhtar Gidado ya ce nadin na da nufin inganta ayyuka, wakilci da tabbatar da gwamnati mai amsa bukatun jama’a daban-daban a Bauchi
  • Wadanda aka nada sun hada da tsofaffin ‘yan siyasa, kuma an zaɓe su bisa cancanta, kwarewa da hangen shugabanci da zai kara inganta jama'a
  • Gwamnan ya bukaci su himmatu wajen bauta wa jama’a, yana fatan za su taimaka wajen samar da ci gaba mai dorewa da kyakkyawar gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rikita jihar da sababbin nade-naden gwamnati.

Gwamna Bala ya amince da nada sababbin masu taimaka na musamman a bangarori da dama har guda 168.

Gwamna ya naɗa hadimai 168 a gwamnatinsa
Gwamna Bala Mohammed ya naɗa hadimai guda 168 a Bauchi. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Asali: Facebook

Gwamna Bala ya nada hadimai 168 a Bauchi

Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a yau Talata a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce hakan na da nufin farfado da aikin gwamnati da kuma kara yawan shigar jama’a cikin mulki.

Gidado ya ce:

“Wadannan nadin na daga cikin kokarin gwamna na tabbatar da shigar da kowa da kowa, inganta ayyuka, da kafa gwamnati mai wakiltar muradun jama’ar Bauchi.
“Sababbin masu taimakon, mafi yawansu tsofaffin masu mukaman siyasa ne a matakin tarayya, jiha da kananan hukumomi, kuma an zabe su ne bisa cancanta da kwarewa.”
Gwamna ya jika yan jiharsa da mukamin hadimai 168
Gwamna Bala Mohammed ya ba da muƙamin hadimai 168 a Bauchi. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Asali: Twitter

Bauchi: Yadda Gwamna Bala ya rarraba muƙaman

Sanarwar ta tabbatar da cewa an zabi mutanen ne bisa tarihi, kwarewa da fahimtar siyasa, kuma ana sa ran za su kawo sababbin dabaru a gwamnati.

Hadimin gwamnan ya mika sakon taya murna na mai gidansa ga sababbin mukarraban, tare da shawartarsu su dauki wannan dama a matsayin kira zuwa ga manyan ayyuka.

Ya jaddada muhimmancin jajircewa, biyayya da sanya muradun jama’a a gaba, domin gwamnati na kara kokarin kawo ci gaba mai amfani ga jama’ar Bauchi.

Gidado ya ce nadin zai fara aiki nan take, kuma gwamna yana da yakinin hakan zai taimaka wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci da ci gaba mai dorewa.

Nade-naden sun hada da manyan mataimaka biyar kan al’amuran siyasa da al’umma, guda daya kan fansho, da manyan mataimaka kan siyasa da al’umma 60.

Haka kuma akwai daya babban mataimaki kan harkokin kwadago, mataimaka na musamman kan siyasa da al’umma 38, da kuma mataimaka na sirri guda 63.

2027: An fara manna fastocin gwamna Bala

Kun ji cewa an fara manna fastocin neman takarar shugaban kasa a 2027 na Gwamna Bala Mohammed a manyan tituna na lungu da sakon jihar Bauchi.

Rahotanni sun ce an hango fostocin a manyan tituna kamar hanyar 'Railway', Sabon Titin Karofi da Kofar Dumi, inda aka manna su a wurare masu jan hankali.

Sai dai ma'abota soshiyal midiya sun yi martani mai zafi game da wadannan fastoci, har wasu ke nuna rashin cancantar gwamnan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.