Bankwana da Siyasa: Shugaban Malamai a Izala, Sheikh Dalha Ya Fita daga APC
- Shugaban malamai a Izala, Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC da harkar siyasa gaba ɗaya
- Sheikh Dalhatu Abubakar ya bayyana cewa sabuwar rawar da yake takawa a matsayin shugaban malamai na ƙasa ne ya sa ya fita a siyasa
- A cikin wata wasikar da ya fitar, shehun malamin ya tabbatar da cewa yanzu ba shi da jam’iyya, ya riga ya zama jagora ga dukkan ‘yan Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Fitaccen malamin addini kuma ɗan siyasa daga jihar Bauchi, Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi Kantana, ya sanar da fita daga APC.
Sheikh Hakimi ya bayyana haka ne cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na mazabar Dull da ke karamar hukumar Tafawa Balewa.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan matsayar da malamin ya yi ne a cikin wani sako da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasikar, Sheikh Hakimi ya ce sabon matsayinsa na shugabancin majalisar malamai ta ƙasa a karkashin kungiyar Izala ne ta sa ya yanke hukuncin barin siyasa.
Sheikh Dalhatu ya karɓi shugabancin Izala ne bayan rasuwar Sheikh Saidu Hassan Jingir, wanda ya shafe shekaru yana jagorantar harkokin addini a Najeriya.
Bayanin Sheikh Dalhatu na fita daga APC
A cikin wasikar da ke ɗauke da kwanan wata 1 ga Mayu, 2025, Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi ya ce:
“Na yanke wannan hukunci ne bisa sabon nauyin da aka daura mani a matsayina na Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Ƙasa na biyu.”
Malamin ya ƙara da cewa ba shi da wata jam’iyya da yake ciki yanzu, ya riga ya zama na kowa da kowa:
“Don haka yanzu ni mai kula da kowa ne a Najeriya, ba ni da wata jam’iyyar siyasa da nake ciki,”
Takarar Sheikh Dalhatu a APC a 2019
Sheikh Hakimi ya fafata a siyasa a shekarar 2019, ya tsaya takarar kujerar Majalisar Wakilai daga yankin Dass/Bogoro/Tafawa Balewa a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Daily Trust ta rahoto cewa malamin bai yi nasara ba a lokacin, inda tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya kayar da shi.
Yakubu Dogara da ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP, ya samu kuri’u 73,609 yayin da Sheikh Hakimi ya samu kuri’u 50,708.

Asali: Facebook
Sai dai duk da rashin nasarar, Sheikh Hakimi ya cigaba da taka rawa a fagen addini da zamantakewa, inda yanzu ya zama ɗaya daga cikin jagororin Izala a matakin ƙasa.
Matashi ya ki karbar mukami a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa a kwanakin baya gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya raba mukamai da dama.
Sai dai cikin wadanda aka ba mukaman akwai wani matashi daga karamar hukumar Katagum da ya ki amsar matsayin.
Mutane da dama a kafafen sada zumunta sun yi mamaki da matashin mai suna Musa Azare ya ki karbar matsayin siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng