An Shiga Yanayin Tashin Hankali da Wani Bam Ya Tashi da Mutane a Jihar Zamfara

An Shiga Yanayin Tashin Hankali da Wani Bam Ya Tashi da Mutane a Jihar Zamfara

  • Rahotanni sun nuna cewa mutane biyu sun mutu bayan wani abin fashewa da ake zargin bam nd ya tashi a hanyar Gurusu-Gwashi ta jihar Zamfara
  • Majiyoyi daga yankin da lamarin da auku sun bayyana cewa ana zargin wani babur ne ya taka bam ɗin da aka binne a ƙasa a Bukuyyum
  • Dakarun rundunar sojoji sun ci gaba da sintiri da mamaye yankin domin hana sake kai makamancin wannan hari da kuma bincike wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Mutane biyu sun rasa rayukansu bayan wani bam da aka dasa, wato IED, ya tashi a hanyar Gurusu-Gwashi da ke ƙaramar hukumar Bukuyyum ta jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:04 na safiyar jiya Laraba, 26 ga watan Augustan 2026, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

Kara karanta wannan

Abin mamakin da Bashir El Rufa'i ke gani idan ya ziyarci babansu da ke tsare

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya Zagazola Makama, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rahoto da ya wallafa a shafinsa na X.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Makama cewa dakarun runduna ta 1 da aka jibge a sansanin FOB da ke Gwashi sun gaggauta mayar da martani bayan samun rahoton fashewar bam ɗin.

Yadda babur ya taka bam a Zamfara

Rahotanni sun ce binciken farko da jami'an tsaro suka gudanar ya nuna cewa wani babur ne ya taka bam ɗin da aka binne a yankin, lamarin da ya haddasa fashewar mai ƙarfi.

A cewar majiyoyin, fashewar bam din ta yi sanadin mutuwar wani namiji da wata mace da ke wurin.

An gano gawarwakin mutanen biyu a wurin da lamarin ya faru, kafin daga bisani a kwashe su zuwa Babban Asibitin Bukuyyum domin gudanar da matakan da suka dace.

Sojoji sun kai dauki cikin gaggawa

Kara karanta wannan

An kashe wani bawan Allah a hanyar dawo wa daga wurin Maulidin Annabi SAW a Kano

Zagazola Makama ya nakalto wata majiya tana cewa jami'an tsaro sun fara gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan yadda aka dasa bam ɗin da kuma waɗanda ka iya kasancewa suna da hannu a lamarin.

Bayan fashewar, dakarun sojin sun ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, inda suka ci gaba da mamaye wurin tare da gudanar da sintiri a kan hanyar da kuma wuraren da ke kewaye.

Matakan na daga cikin ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi na hana sake kai hare-hare da kuma hana 'yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuffika samun damar gudanar da ayyukansu a yankin.

Sojoji.
Dakarun sojojin Najeirya suna ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro Hoto: @zagazolamakama
Source: Twitter

Hare-haren bam sun ƙaru a Zamfara

Jihar Zamfara, wadda ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, ta fuskanci hare-haren 'yan bindiga da kuma amfani da na'urorin fashewa a wasu hanyoyi da yankunan karkara.

Hare-haren bam na daga cikin barazanar da ke jefa tsoro a zukatan mazauna yankunan, musamman matafiya da jami'an tsaro da ke amfani da hanyoyin da ke tsakanin garuruwa da ƙauyuka.

A watan Yuni, wasu jami'an 'yan sanda uku sun rasa rayukansu bayan wani bam na IED ya tashi a hanyar Anka zuwa Bagega, a ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano

Sojoji sun ceto mutane a Zamfara

Kun ji cewa Sojojin Operation Fansan Yamma sun kubutar da wasu bayin Allah, daga cikinsu har da jariri, daga hannun ’yan bindiga da suka kai wani hari a Zamfara.

An kuma bayyana cewa mata biyu sun samu raunukan harbin bindiga a lokacin harin, kuma an garzaya da su asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262