Abun Al Ajabi
Gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu wanda ya kasance dan kirista ya burge yan Najeriya da dama yayin da aka gano shi yana karanta Fatiha a wani bidiyo.
Fitaccen attajirin ‘dan kasuwar Najeriya, Femi Otedola, ya fitar da zunzurutun kudi har N1.4 biliyan inda yayi hayar katafaren jirgin ruwa domin shagalin bazde.
Wani mai amfani da Twitter mai suna Vulfang Nwaru ya nuna damuwarsa bayan diyarsa ta shiga madafi sannan ta fasa tulin kwai har kiret daya. Hotunan sun yadu.
Wata babbar kotun yanki dake Karu a Abuja ta gurfanar da wani Okechukwu Eze mai shekaru 37 kan zargin cin zarafin wata mata tare da janyo zubewar cikin jikinta.
Bayan tsawon shekaru da dama tana jiran tsammani, Allah ya albarkaci wata yar Najeriya mai suna Chinwe Mbahotu da haihuwar yan uku, maza biyu da mace daya.
Wata matashiya ta tsinci kanta a halin kunar zuciya bayan ta gano cewa uban ‘ya’yanta na soyayya da mahaifiyarta. Ta saki hirarsu yayin da ta sallama uwar tata.
Babbar kotun jihar Bauchi ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani matashi mai suna musa Hamza bayan ta same shi da hannu a kisan wani abokinsa.
Wata matashiyar budurwa mai shekaru 40 a duniya ta shiga damuwa inda ta garzaya shafukan soshiyal midiya don kokawa kan rashin samin tsayyayen namijin aure.
An gano cewa, kafar sada zumuntar zamani ta Twitter tana da niyyar kallafawa jama’a harajin $20 amma ga duk masu asusun da aka tantance daga watan Nuwamba.
Abun Al Ajabi
Samu kari