Kotu Ta Umarci a Rataye Wani Mutumi Sakamakon Halaka Abokinsa a Bauchi

Kotu Ta Umarci a Rataye Wani Mutumi Sakamakon Halaka Abokinsa a Bauchi

  • Kotu ya yi umurnin kashe Musa Hamza ta hanyar rataya bayan ta same shi da hannu a kan kisan abokinsa
  • Mai shari’a Faruq Umar Sarki na babbar kotun jihar Bauchi ne ya zartar da wannan hukunci bayan matashin ya amsa laifinsa
  • Justis Sarki ya ki amsar rokon mai laifin na neman ayi masa sassauci idan ya yi umurnin rataye shi don zama izina ga sauran mutane

Bauchi - Wata babbar kotun jihar Bauchi ta yankewa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kashe abokinsa mai shekaru 17, Nigerian Tribune ta rahoto.

Mai shari’a Faruq Umar Sarki ya yankewa mutumin mai suna Musa Hamza hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da aikata laifin da ake tuhumarsa a kai na kashe abokinsa.

Justis Sarki ya yanke hukuncin ne bayan ya kama Hamza da laifin yanka wuyar abokin nasa inda ya cire kwayar idanunsa biyu ya kuma sakasu cikin kwalba kafin ya binne kai da gangar jikin a wurare daban-daban.

Sandar kotu
Kotu Ta Umarci a Rataye Wani Mutumi Sakamkom Halaka Abokinsa a Bauchi Hoto: THISDAYLIVE
Asali: UGC

Lauyoyi daga ma’aikatar shari’a da suka hada da Mohammed Y Ibrahim, Salihu A Haruna da Ali S Yusuf sun shigar da kara a kan wanda aka yankewa hukuncin inda suka zarge shi da aikata kisan kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukuncin laifin na shine kisa kamar yadda sashi na 221 na dokar Penal Code ya tanadar.

Masu karar sun sanar da kotu cewa Hamza daga karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi ya ja abokinsa mai shekaru 17 mai suna Adamu Ibrahim zuwa wani jeji da ke kusa.

Da suka isa wajen kuma ya ga babu idon mutane, sai ya make shi da sanda, ya yanke mai kai, ya kwakule idanunsa biyu sannan ya binne kan da gangar jikin a wurare daban-daban.

Da farko wanda ake zargin ya karyata tuhumar da ake masa a gaban kotu a lokacin da aka fara shari’ar, amma daga baya ya amsa laifinsa.

Mai gabatar da karar ya gabatar da shaidu shida a gaban kotun don kafa hujja yayin da wanda ake karar ya gabatar da shaida daya wato shi kansa da ake tuhuma.

Shaidun sun bayyana cewa mahaifin yaron ya kai korafin cewa dansa bai dawo gida ba a wannan ranar, amma ya ji cewa an gan shi tare da wanda ake zargin kuma cewa sun fita tare, su uku a wannan daren kuma sun ci abinci dare tare.

Sun kara da cewar fada bai shiga tsakaninsu ba, kuma basu zagi junansu ba, daga bisani sai daya daga cikinsu ya tafi ya bar wanda ake zargin tare da mamacin, amma da aka tambayi mai laifin sai yace shima ya tafi ya bar shi.

Sai dai bayan an kama shi, yan sanda sun je daikinsa don bincike inda suka samu waya da layin waya na mamacin a wajensa, da aka ga wayar a hannun mai laifin, sai aka ci gaba da bincike sannan ya amsa laifinsa.

Ya ce ya kai mamacin jej sannan ya kashe shi ya kuma yanke masa kai, ya kwakule idanunsa biyu, ya kuma kai yan sandan zuwa wajen da ya binne gawar mamacin.

Da aka tambaye shi inda idanun suke, sai yave ya barsu a gida saboda ya saka idanun a cikin wata kwalba.

Yan sanda sun dauki idanu da gawar mamacin zuwa babban asibitin Alkaleri inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Duk kokarin lauyan wanda ake zargi, Mahmud Maidoki na kare shi ya ci tura.

Da yake zartar da hukunci, alkalin kotun, ya bayyana cewa bisa ga jawaban shaidun da kuma na wanda ake zargin, kotu ta kama shi da laifin saboda wanda ake zargin ya aikata kisan kai da gangan.

Justis Faruq ya kuma ki amincewa da bukatarsa na yi masa sassauci sannan ya yanke masa hukuncin kisan kai ta hanyar rataya daidai da sahi 273 da 221 na dokat Penal code don zama izina ga wanda ke da niyan aikata irin laifin.

Ifeanyi: Yan Sanda Sun Kama Ma’aikatan Mawaki Davido Gaba Daya Kan Mutuwar Dansa

A wani labarin, mun ji cewa yan sanda sun kama dukkanin ma’aikatan gidan shahararren mawakin Najeriya, Davido kan mutuwar dansa, Ifeanyi.

Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da cewar dukkanin ma’aikatan na tsare a hannunsu don amsa tambayoyi, Sahara Reporters ta rahoto.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Lagas, Ben Hundeyin, ya fadama manema labarai a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba cewa ana nan ana gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a mutuwar yaron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel