Shugaban Kasa Musulmi Ya Fara Yaki da Addini, Ya Hana Mata Sa Hijabi

Shugaban Kasa Musulmi Ya Fara Yaki da Addini, Ya Hana Mata Sa Hijabi

  • Gwamnatin Azerbaijan ta amince da wani sabon tsari da ya hana ɗalibai da malamai sanye da hijabi a makarantu, lamarin da ya jawo zanga-zanga
  • An fara hana wasu ɗalibai da malamai shiga ajujuwa saboda sanye da hijabi, yayin da wasu ɗalibai suka kaurace wa karatu domin nuna adawa da matakin
  • Matakin ya kuma jawo martani a Turkiyya, inda masu zanga-zanga suka bukaci gwamnatin Azerbaijan ta sake duba dokar da ta shafi mata Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani sabon matakin gwamnatin Azerbaijan da ya takaita sanya hijabi a makarantu ya jawo ce-ce-ku-ce da zanga-zanga, yayin da ake ci gaba da nuna adawa da dokar a cikin kasar da ma wajenta.

Gwamnatin ta amince da gyaran dokar sanya tufafin makaranta a watan da ya gabata, inda ta haramta tufafin da ta ce sun saɓa wa tsarin zaman duniya, ba tare da ambaton hijabi kai tsaye ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Mutane da dama sun mutu yayin da suka je ɗibar ganima jikin wata tankar fetur

Shugaban Azerbaijan a wajen taro
Shugaban Azerbaijan, Ilham Aliyev. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta rahoto cewa an fara hana wasu malamai da ɗalibai shiga makarantu saboda sanya hijabi, lamarin da ya haifar da fushi da nuna rashin amincewa da sabon tsarin.

An hana sa hijabi a Azerbaijan

Gwamnatin kasar ta bayyana cewa an yi gyaran dokar ne domin tabbatar da tsarin sanya tufafi iri ɗaya a makarantu, wanda zai dace da tsarin zaman duniya na kasar.

Kusan kashi 96 cikin 100 na al'ummar Azerbaijan Musulmai ne. Duk da haka, kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana ta a matsayin kasa mai bin tsarin duniyanci, tare da tabbatar da 'yancin addini.

Sabon tsarin ya kuma tanadi cewa za a iya sanya tufafin da ke nuna tarihi, al'adu da dabi'un al'ummar Azerbaijan a bukukuwa, matuƙar majalisa ta amince da su.

Majalisar tana aiki ne ƙarƙashin Ma'aikatar Kimiyya da Ilimi ta kasar. Gwamnatin ta ce tsarin tufafin zai taimaka wajen tabbatar da ƙwarewar malamai da kuma kyautata martabar makarantu.

Kara karanta wannan

Kisan Ayatollah Ali Khamenei ya damu Trump, ya nuna alamun nadama

An fara zanga-zanga

Matakin ya jawo zanga-zanga da yaƙin neman goyon baya a kafafen sada zumunta a Azerbaijan. Wasu bidiyo da suka bazu sun nuna ɗalibai suna rungumar malamansu tare da kuka yayin da aka hana su shiga makarantu.

Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa ɗalibai a aƙalla makarantu biyu sun kaurace wa karatu domin nuna adawa da takunkumin.

Haka kuma, ɗan jaridar da ke tsare, Polad Aslanov, ya fara yajin cin abinci domin nuna rashin amincewarsa da sabon tsarin.

Aslanov, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru 113 bayan an same shi da laifin cin amanar kasa a shekarar 2020, ya bayyana cewa yana amfani da hanyar da yake da ita wajen nuna adawa da take haƙƙoƙin kundin tsarin mulki.

Turkiyya ta shiga cikin lamarin

India Today ta wallafa cewa adawar da aka fara yi a Azerbaijan ta bazu zuwa Turkiyya, inda aka gudanar da zanga-zanga tare da yaƙin neman goyon baya a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Badakalar makamai: Buratai ya fadi wadanda aka tura wa makudan kudi

Wasu sun kwatanta matakin da halin da Turkiyya ta shiga a shekarar 1997, lokacin da aka hana mata masu hijabi shiga azuzuwan jami'o'i, yayin da aka sallami wasu ma'aikatan gwamnati ko aka tilasta musu yin murabus saboda sanya hijabi.

A makon da ya gabata, masu zanga-zanga sun taru a wajen ofishin jakadancin Azerbaijan da ke Istanbul, inda suka bukaci hukumomin Baku su sake duba matakin da ya shafi matan Musulmi.

Shugaban Azerbaijan, Ilham Aliyev, ya yi suka a kaikaice kan zanga-zangar da ake yi a Turkiyya, duk da cewa kasashen biyu abokan hulɗa ne na kut-da-kut.

Zanga-zangar Azerbaijan
Masu zanga zanga kan hana hijabi a Azerbaijan. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wani jawabi da ya yi a taron jam'iyyarsa ta New Azerbaijan, Aliyev ya yi gargaɗin cewa kada a yi katsalandan a salon rayuwar al'ummarsa, ba tare da ambaton Turkiyya kai tsaye ba.

Sakataren SCSN ya rasu

A wani labarin, an ruwaito cewa babban sakataren majalisar koli ta Shari'a ta Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba-Ahmed, ya rasu.

Marigayin, wanda malamin addinin Musulunci ne kuma mai fafutukar tabbatar da adalci, ya shafe rayuwarsa wajen hidimtawa Musulunci da bil'adama.

Manyan malamai a fadin Najeriya da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sun bayyana shi a matsayin mutum mai haɗa kan al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng