Asiri Ya Tonu: An Kama Wasu Matasa 2 da ba a Yi Tsammani ba Dauke da Bindiga a Kano

Asiri Ya Tonu: An Kama Wasu Matasa 2 da ba a Yi Tsammani ba Dauke da Bindiga a Kano

  • Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wasu matasa biyu masu shekaru 19 bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba
  • An kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin a Hotoro, inda aka gano bindiga karama da harsasai biyu a hannunsa
  • Kwamishinan ’yan sanda ya bayar da umarnin zurfafa bincike, bayan haka za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wasu matasa biyu masu shekaru 19 bisa zargin mallakar makamin bindiga ba bisa ƙa’ida ba.

Dakarun yan sanda sun kwato bindiga ƙirar Pistol da aka ƙera a gida tare da harsasai biyu masu rai daga hannun wadanda ake zargi.

CP Bakori.
Kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori a ofishinsa Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Manyan yan sanda sun shiga matsala bayan yan kungiyar asiri sun gyara caji ofis

Yadda aka kama matashi da bindiga

A cewar sanarwar, jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi na farko, Rufai Ahmed, mazaunin unguwar Hotoro da ke Kano, a ranar 11 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 10.30 na dare.

An kama shi ne ta hannun wata tawagar jami’an sa ido da ke aiki ƙarƙashin sashen ’yan sanda na Farm Centre.

Tawagar ta tare wata keke mai ƙafa uku da ake kira Keke NAPEP a kan titin Sokoto a yayin wani sintiri da aka gudanar bisa bayanan sirri.

Bayan gudanar da bincike a wurin, jami’an sun gano wata jaka ɗauke da bindiga da aka ƙera a gida da harsasai biyu a hannun Ahmed, inda suka kama shi nan take.

An kama wanda ake zargi na 2

Bayan Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bada umarnin gudanar da binciken sirriz jami’an sashen binciken manyan laifuffuks sun kama wani matashi, Aliyu Ibrahim, mai shekaru 19, mazaunin unguwar Kawo da ke Kano.

Kara karanta wannan

An kai ɗan Najeriya kotu kan ikirarin mallaka da shirin cefanar da jirgin sojoji

An kama Ibrahim ne bisa alaƙarsa da wannan batu ka mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba.

Za a gurfanar da su a kotu

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano ya bayar da umarnin ƙara zurfafa bincike kan lamarin, bayan kammala shi kuma a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

CP Bakori ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa lura da ƙwarewarsu, yana mai jaddada ƙudirin rundunar na yaƙi da kwace makamai ba bisa ƙa’ida ba da sauran ayyukan ta’addanci a faɗin jihar Kano.

Haka kuma, ya buƙaci al’umma da su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen hana aikata laifuka da gano waɗanda ke aikata su.

Yan sanda sun hana taron TMG a Kano

Kun ji cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi magana kan dalilin da ya sa jami’ansa suka tare wurin taron masu adawa da Shugaba Tinubu a Kano

Bakori ya ce ’yan kungiyar Tinubu Must Go suna da ’yancin gudanar da taronsu, amma sanar da ’yan sanda zai taimaka wajen tabbatar da tsaronsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262