Dan APC Ya Fito Yana Goyon Bayan Atiku, zai Yi wa Tinubu Ungulu da kan Zabo

Dan APC Ya Fito Yana Goyon Bayan Atiku, zai Yi wa Tinubu Ungulu da kan Zabo

  • Wani ɗan jam'iyyar APC, Chidozie Victor Anuebunwa, ya bayyana cewa ya shiga tsarin haɗin gwiwa da jam'iyyar ADC domin marawa Atiku Abubakar baya a zaɓen 2027
  • A cewarsa, siyasa ta haɗaka da saɓa wa ra'ayin jam'iyya ba sabon abu ba ne, kuma ana karɓar hakan hannu biyu-biyu a halin yanzu
  • Anuebunwa ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 16 ga watan Okutoba, 2026, yayin da yake mayar da martani mai ƙarfi kan rikicin siyasar cikin gida da al'amuran da ke faruwa a faɗin ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani jigo kuma ɗan jam'iyyar APC mai mulki, Chidozie Victor Anuebunwa, ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, domin zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da tsagerun 'yan bindiga, an ceto mata bayan zubar da jini

Anuebunwa ya bayyana cewa duk da kasancewarsa ɗan APC, yana gudanar da harkokin siyasa ne ƙarƙashin tsarin haɗaka domin tabbatar da nasarar jam'iyyar adawa ta ADC.

Chidozie Victor Anuebunwa da Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a hagu da Chidozie Victor Anuebunwa a dama. Hoto: Chidozie Victor Anuebunwa|Atiku Abubakar
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, Anuebunwa ya jaddada cewa ba zai sauya matsayarsa ba saboda neman abinci ko alfarmar siyasa daga wani.

Chidozie ya goyi bayan Atiku

Anuebunwa ya ƙara da cewa sakonsa na baya-bayan nan ya sami karɓuwa sosai inda sama da mutane 83,100 suka karanta shi cikin ƙasa da sa'o'i 24, yana mai cewa mutane da dama sun yarda da matsayarsa.

Ya rubuta cewa:

"Ina ɗan APC, amma ina cikin haɗakar haɗin gwiwa da ADC. A jam'iyyata ta APC, an yarda da rashin biyayya ga jam'iyya; ana yaba shi sosai. Jama'a ku tashi ku zabi Atiku! Maganar gaskiya kenan,"

Matsayarsa game da Wike

Anuebunwa ya kuma mayar da martani ga waɗanda ke neman ɗaukin kuɗi daga gare shi bisa kuskuren tunanin yana da alaƙa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Ya bayyana cewa ba zai taɓa rusuna wa Ministan na Tarayya ba saboda neman abinci, yana mai jaddada cewa zai fi kyau ya sha garin kwaki da ruwa fiye da ƙasantar da kansa domin samun abinci.

Kara karanta wannan

Yadda uwa ta sayar da jaririyarta Naira miliyan 2 wata 1 bayan haihuwa

"Dukkanku ku kuka sani cewa na bayyana matsayata a fili: Ba zan goyi bayan ko rusuna wa Nyesom Wike ba.
Nyesom Wike da Bola Tinubu
Nyesom Wike na gaisawa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

ADC ta soki Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar ADC ya soki Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kan kiran da ya yi wa Atiku Abubakar na ya janye wa Peter Obi.

Sakataren Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana a ranar Juma'a cewa kiran da Kwankwaso ya yi abin kunya ne da ya nuna yana goyon bayan Tinubu.

Ologbondiyan ya jaddada cewa Atiku Abubakar shi ne amintaccen ɗan takarar da jam'iyyar ADC ta tsayar domin ƙalubalantar jam'iyyar APC mai mulki, kuma ba zai janye wa kowa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng