Ina Addu’a Kada Allah ya Bani Haihuwa, Yara Dawainiya ne: Budurwa a Bidiyo

Ina Addu’a Kada Allah ya Bani Haihuwa, Yara Dawainiya ne: Budurwa a Bidiyo

  • Wata kyakyawar budurwa ‘yar Najeriya mai suna Notzarraabba ta bayyana dalilin da yasa bata son haihuwa kwata-kwata
  • Kamar yadda tace, bata tunanin zata taba haihuwa nan gaba koda yaro daya ne kuwa saboda yara dawainiya ce kawai
  • A yayin martani kan bidiyon da ta wallafa a TikTok, jama’a da yawa sun dinga sukarta kan cewa wannan hukuncin da ta yanke bai yi ba

Wata budurwa ‘yar Najeriya tace bata hango kanta matsayin wacce zata haifa yara nan gaba saboda bata kaunar yara a bidiyo.

Kamar yadda tace, tana mamaki idan ta ga mace tana son yara da irin kaunar da take nuna musu.

Budurwa mara son haihuwa
Ina Addu’a Kada Allah ya Bani Haihuwa, Yara Dawainiya ne: Budurwa a Bidiyo. Hoto daga TikTok/Notzarraabba
Asali: UGC

Ta bayyana cewa yara dawainiya ne kawai gareta kuma kafin ta auri mutum, za ta tabbatar da cewa ya san da akidarta na rashin son haihuwa.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Baro Dubai Zuwa Najeriya Saboda Bikin Kawarta, Ta Gano Ashe Saurayinta Zata Aura

A kalamanta:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Kun san yadda mata suke son zama uwaye tare da haihuwar yara kamar 15. Ni dai a wurina a’a, bana kaunar yara. Ina jin cewa wata damuwa ce wacce mutum bai dace ya fuskanta ba. Dawainiya ce kuma. A gaskiya bana tsammanin zan taba haihuwa.
“Kafin in yi aure, zan sanar da mijina cewa bana son yaro ko daya. Babu dalilin da zai sa in haihu. Kawai bana bukatar yara.”

Soshiyal midiya tayi martani

@namama.1 yace:

“Babu abinda ki ka yi ba daidai ba, ina ma iyayen ki sun san wannan tun farko kafin haihuwar ki. Da basu haifa jaka mummuna mace irin ki ba.”

@for.hanadra yace:

“Bayyana ra’ayin ki ba laifi bane, amma da kin bar wannan a cikin zuciyar ki tunda baki san inda zai kare ba.”

Kara karanta wannan

Kebera yake sha? Bidiyon mataccen takalmin da wani ya saka ya je neman aure ya ba mamaki

@hikmagil ya rubuta:

“Mutane suna cewa da izinin Allah ba zaki samu ko daya ba, kada ki manta yayin da ki ke addu’a mai kyau ko akasin hakan, tana dawo miki ne.”

@eyshaluv1 ta kada da cewa:

“Subhanallah ina son yara, ya Allah ka albarkace ni da yara. Don Allah ku saka ni a addu’a, ina son su yanzu shekaru na 6 da aure.”

@khadijaluv tace:

“Na yadda kuma na fahimce ki, shekarun ki ne kawai ke magana. Zan so sanin yadda za ki ji idan ki ka shekara uku da aure babu haihuwa.”

Kalla bidiyonta:

Asali: Legit.ng

Online view pixel