Ana Fargabar Juyin Juya Hali da Mummunan Zanga Zanga Ta Barke a Tunisia

Ana Fargabar Juyin Juya Hali da Mummunan Zanga Zanga Ta Barke a Tunisia

  • Dubban 'yan Tunisiya sun gudanar da zanga-zanga kan matsin tattalin arziki, inda suka buƙaci Shugaba Kais Saied ya sauka daga mulki
  • Masu zanga-zangar sun zargi gwamnatin Saied da raunana dimokuraɗiyya, gazawa magance matsalolin tattalin arziki
  • Ƙungiyoyin adawa, lauyoyi, likitoci da ’yan jarida sun shiga zanga-zangar, suna buƙatar sakin masu sukar shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tunis, Tunisia - Dubban ’yan ƙasar Tunisiya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar kan Shugaba Kais Saied, sakamakon ƙara taɓarɓarewar matsalolin tattalin arziki a ƙasar.

Masu zanga-zangar sun kuma buƙaci Saied ya yi murabus, inda suka zargi gwamnatinsa da raunana dimokuraɗiyya da kuma gazawa wajen magance matsalolin tattalin arzikin ƙasar da ke ƙara taɓarɓarewa.

An yi zanga-zanga a Tunisia
Shugaban kasar Tunisia, Kais Saied a masarauta da ke birnin Brussels a Belgium a 2021. Hoto: Olivier Matthys.
Source: Getty Images

Musabbabin ɓarkewar zanga-zanga a Tunisia

Ƙungiyar ƙwadago ta UGTT da ƙungiyoyin farar hula ne suka jagoranci zanga-zangar, wadda ta gudana a daidai lokacin da ayyukan jama'a ke tabarbarewa, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Yan takarar gwamnan jam'iyyar adawa sun fadi wanda za su yi a zaben shugaban kasa

Zanga-zangar ta haɗa ƙungiyoyin adawa daga ɓangarorin siyasa daban-daban, a wani yanayi da ba kasafai ake gani ba na haɗin kai, bayan shekaru da dama na saɓanin cikin gida sun raunana ikonsu na tattara jama'a masu yawa.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar, ciki har da ’yan siyasar adawa, lauyoyi, likitoci, ’yan jarida da marasa aikin yi, sun yi tattaki a titin Habib Bourguiba da ke birnin Tunis, babban birnin ƙasar.

Wannan titi na daga cikin muhimman wuraren da aka gudanar da zanga-zangar shekarar 2011, wadda ta taimaka wajen haifar da tarzomar da aka fi sani da Arab Spring a ƙasashen Larabawa.

Matakin da yan sanda suka ɗauka

An tura ɗaruruwan jami'an ’yan sanda zuwa sassa daban-daban na babban birnin, yayin da masu zanga-zangar ke rera taken, “Ba mu tsoro, iko na hannun jama'a yake” da kuma “Gidajen yari sun cika, mutane na fama da yunwa.”

Sun buƙaci a saki masu sukar shugaban ƙasa da ake tsare da su, tare da yin Allah-wadai da abin da suka bayyana a matsayin hare-hare kan haƙƙin ƙungiyoyin ƙwadago.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka hana Atiku, Obi da sauransu haduwa su kifar da Tinubu

Wasu masu zanga-zangar sun ɗauki allunan da ke nuna matsalar rashin aikin yi da kuma gurɓacewar muhalli.

Ana neman shugaban Tunisia ya yi murabus
Shugaban kasar Tunisia, Kais Saied yayin taro a birnin Brussels a Belgium. Hoto: Olivier Matthys.
Source: Getty Images

Yaushe Saied ya kwace iko a Tunisia

A shekarar 2021, Saied ya ƙwace iko a kasar Tunisia inda ya rusa majalisar dokoki tare da sallamar alƙalai da dama, kafin ya fara mulkin ƙasar ta hanyar dokokin da yake bayarwa kai tsaye.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun kuma zargi gwamnatinsa da ƙara tsaurara matakan murƙushe ƙungiyoyin farar hula, ’yan jarida da kuma ’yan siyasar adawa.

Sai dai Saied ya ƙi amincewa da waɗannan zarge-zarge, yana mai jaddada cewa shi ba azzalumin shugaba ba ne, cewar Vanguard.

Ya kuma zargi abokan hamayyarsa da ƙoƙarin haddasa matsalolin tattalin arziki da gangan domin tayar da hankulan jama'a.

Shugaban ƙasar ta Arewacin Afirka ya hau mulki a shekarar 2019, kuma ya shafe shekaru bakwai yana jagorantar ƙasar.

Gwarzo: Yan Kwankwasiyya sun yi zanga-zanga

A baya, an ji cewa magoya bayan Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano, suna neman INEC ta dawo da sunan ɗan takarar gwamnan NDC.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun maida martani da Tinubu ya ce ba zai iya zuwa kamfe wasu jihohi ba

Mataimakin ɗan takarar mataimakin gwamna na NDC, Mustapha Rabiu Kwankwaso ne ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa ofishin INEC.

Kwankwasiyya ta zargi wani ma’aikacin INEC da hannu wajen amfani da takardun da ake zargin an ƙirƙira sa hannun bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.