Budurwa Ta Yada Bidiyon Kalan Takalmin da Saurayinta Yazo Dashi Neman Aurenta

Budurwa Ta Yada Bidiyon Kalan Takalmin da Saurayinta Yazo Dashi Neman Aurenta

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta karbi bakuncin wani manemin aurenta da ya zo takanas don ganin iyayenta
  • Sai dai, bai burge ta ba, domin kuwa wani nau'in takalminsa da ta yada a wani bidiyo ya nuna irin halin da yake ciki
  • Yayin da ta yada bidiyon, jama'a da dama sun yi ca, sun bayyana yadda suka ji da ganin wannan takalmi matacce

Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna @black.teenah ta yada bidiyo mai ban dariya na wani manemin aurenta.

Kamar yadda ya bayyana, mutumin ya zo gidan su budurwar ne domin neman aurenta.

Takalmin saurayin wata ya ba da mamaki
Budurwa Ta Yada Bidiyon Kalan Takalmin da Saurayinta Yazo Dashi Neman Aurenta | Hoto: @black.teenah/TikTok
Asali: UGC

Yayin da ya cire takalminsa ya shiga gidan su Teenah, ta kadu bayan ganin irin takalmin da ya zo dashi.

Ta dauki bidiyonsa, kana ta yada shi a kafar TikTok, inda ta bayyana wani mataccen takalmi na mutumin da ke son aurenta.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon da ta yada:

Martanin jama'ar TikTok

@ifeakajay yace:

"Idan aka binne shi a kasa, wannan abu ai sai ya koma taki."

@gloglit yace:

"Ina nema miki tsari da wannan ooooo."

@amawendell yace:

"Yariman ya yi shigan 'yan acaba domin ya nemi gimbiyarsa."

@princessamira250 yace:

"Ina ga fa attajiri ne. Kawai ya boye kansa ne domin ya samu soyayyar gaskiya don Allah kada ke tsallake wannan dama, ki amince kawai."

@ritajonas6 yace:

"Watakila yarima ne ya shigar bultu. Ban san ko irin abin da nake gani a fina-finan Najeriya bane."

@perryprechz yace:

"Kawai ki aure shi, ba kudi bane ke nufin komai ba. Watakila ma yana da kudade a boye."

@user3529678170255 yace:

"Bana son mutane masu dabi'a irin ta ki ba."

'Yan N500 da Aka Buga Shekaru 15 da Suka Gabata Sun Bayyana a Yayin da CBN Ke Shirin Sake Fasalin Kudi

Kara karanta wannan

Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Yadda Ango Ya Goyo Amaryarsa A Babur Zuwa Wajen Daurin Aurensu Ya Ja Hankali

A wani labarin, gabanin shirin gwamnatin Najeriya na sauya fasalin N200, N500 da N1000, 'yan Najeriyan da suka boye kudi sun fara ciro abin da suka boye.

A ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, 'yan Najeriya suka fara gano sabbin 'yan N500 kal da aka buga tun shekarar 2007.

Kudin da aka gani, babban bankin Najeriya ne ya buga shi tun 2007, shekaru shida kenan bayan kirkirar gudan N500 a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel