Yan Sanda Zan Kira: Magidanci Ya Koka A Intanet Bayan Karamar Diyarsa Ta Fasa Kwai Kaya Daya

Yan Sanda Zan Kira: Magidanci Ya Koka A Intanet Bayan Karamar Diyarsa Ta Fasa Kwai Kaya Daya

  • Wani magidanci ya nuna rashin jin dadinsa a Twitter bayan karamar diyarsa ta fasa kiret daya a lokacin da saci jiki ta shiga madafi
  • Cikin fushi, mahaifin nata mai suna Vulfang Nwaru ya tambaya ko akwai makarantar kwana ta kananan yara da zai iya sakata
  • Masu amfani da Twitter sun je sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu kan abun da yarinyar tayi

Masu amfani da Twitter sun nuna kaduwa bayan wata karamar yarinya ta fasa kwai kiret daya a madafin mahaifiyarta.

Vulfang Nwaru ya yada hotunan yarinyar tana kallon aika-aikar da tayi bayan gama fasa kwayayen.

Karamar yarinya ta fasa kwai
Yan Sanda Zan Kira: Magidanci Ya Koka A Intanet Bayan Karamar Diyarsa Ta Fasa Kwai Kaya Daya Hoto: @VulfgangNwaruh.
Asali: Twitter

Vulfang ya nuna fushinsa sannan ya tambaya ko akwai makarantar kwana da zai iya saka diyar tasa.

Ya ce idan har akwai irin makarantar, ba zai damu ba zai dunga ware lokaci yana ziyartanta duk karshen mako.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na nuna ya gaji da barna da kiriniyar yarinyar a gida.

Ya rubuta:

"Akwai wata makarantar kwana a kusa? Zan dunga kai mata ziyara duk karshen mako, ban damu ba."

Kalli cikakkiyar wallafar tasa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Orji_vee ta ce:

A yar karamar muryarta "wai zolayata kake yi ne."

@Loud_life9 ya yi martani:

"Kwai kiret daya a wannan lokaci na yunwa dan Allah nemo mata aikin albashi ta fara zuwa aiki."

@miriamifeoma2 ta ce:

"Abu guda da fasasshen kwai shine sai ka bi duk lungu da sako ka goge, idan ba haka ba gida ya dunga wari kamar salga. Yara basu da kyau."

@IAMMILES_D ya ce:

"Na rantse, yan sanda zan kira. Yara basu da kirki wallai. Aikin goge wurin ne yafi damuna wallai. Kawai daukar kayana zan yi, zan nemi matata, kawai ji zata yi mutum ya rufe kofa. Daga bakin kofa zan fara ihun, zo ki ga abun da diyarki tayi fa."

Kara karanta wannan

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

Budurwa Ta Sallamawa Duniya Mahaifiyarta Bayan Ta Gano Tan Soyayya Da Saurayinta

A wani labari na daban, bayan ta gano cewa an yi wasa da hankalinta, wata matashiya ta saki hotunan hirarsu da uban 'ya'yanta da mahaifiyarta.

Matarshiyar mai suna @ChinChillaaaa_, ta bayyana a Twitter cewa ta gano saurayinta yana kwana a gidan mahaifiyarta harma yana da sifiyar makulen gidan.

A cewarta, hakan ya bata mamaki ganin cewa saurayin nata na da nashi gidan da mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel