'Trump Ya Mika Wuya' ga Putin bayan Janye Takunkumi ga Rasha
- laShugaban Amurka, Donald Trump, ya yi amfani da ikon shugabanci wajen dakatar da wasu takunkuman da Majalisar Dokokin Amurka ta amince da su kan Rasha saboda yaƙin Ukraine
- Trump ya bayyana cewa dakatar da wasu daga cikin takunkuman ya dace da muradun ƙasarsa, duk da cewa shi ne ya sanya hannu kan dokar a watan Satumba
- Matakin ya jawo suka daga wasu ’yan majalisar Amurka, yayin da ake zargin Trump da sassauta matsin lamba kan Moscow a lokacin da ake ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi wajen hana aiwatar da wasu takunkuman da Majalisar Dokokin Amurka ta amince da su kan Rasha saboda yaƙin da take yi da Ukraine.
A cikin wani umarnin shugaban ƙasa da ya fitar a daren Juma’a, Trump ya ce dakatar da wasu daga cikin takunkuman ya dace da muradun ƙasar Amurka.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa sabuwar dokar dai ta kamata ta fara aiki ranar Lahadi, bayan Trump ya sanya mata hannu a watan Satumba.
Donald Trump ya cire takunkumin Rasha
Dokar takunkuman, wadda aka sanya wa sunan marigayi Sanatan jam’iyyar Republican daga South Carolina, Lindsey Graham, ta tanadi matakan matsin lamba kan tattalin arzikin Rasha.
Dokar ta bai wa Trump babban iko na kakaba harajin kwastam da zai kai kashi 100 kan manyan ƙasashe biyar da ke sayen man fetur da iskar gas na Rasha, ciki har da China da Indiya.
CNN ta wallafa cewa dokar ta tanadi takunkumai kan Shugaban Rasha, Vladimir Putin, manyan jami’an gwamnatin ƙasar, bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi.
Haka zalika ta shafi jiragen dakon mai da ake zargin Rasha na amfani da su wajen kauce wa takunkuman da aka riga aka kakaba mata.
’Yan majalisa sun matsawa Trump
Kwana biyu kafin matakin Trump, wasu ’yan majalisar Amurka 20 daga jam’iyyun Republican da Democrat sun aika masa da wasiƙa suna neman ya aiwatar da dokar yadda ya kamata.
A wasiƙar da suka fitar ranar Alhamis, sun gode masa bisa sanya hannu kan dokar, amma suka buƙaci ya tabbatar da cikakken aiwatar da ita ba tare da jinkiri ba.
Sun bayyana cewa aiwatar da takunkuman zai taimaka wajen tilasta wa Putin ɗaukar tattaunawar zaman lafiya da muhimmanci.
Sai dai wasu ’yan jam’iyyar Democrat sun soki matakin Trump. Dan majalisa Don Beyer daga jihar Virginia ya zarge shi da sassautawa Moscow da kuma juya wa Ukraine da shugabanta, Volodymyr Zelensky, baya.

Source: Getty Images
Beyer ya ya sanar da cewa matakin Trump ya sake nuna yadda yake mika wuya ga Putin, tare da yin watsi da manufar Majalisar Dokoki na hukunta Rasha saboda yaƙin da ta fara ba bisa ƙa’ida ba.
Amurka za ta farmaki kasar Iran
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Amurka ta tsara sababbin dabarun kai hare-hare kan Iran, ciki har da yiwuwar amfani da babban bam ɗinta da ba ta ɗauke da makamin nukiliya.
Bam ɗin, mai suna MOAB, shi ne mafi girman bam marar makamin nukiliya da Amurka ke da shi. Amfani da shi a yaƙin Iran zai zama babban ƙarin tsananta hare-haren.
Trump na fuskantar matsin lamba na kawo ƙarshen yaƙin da jama’a da dama ba sa goyon bayansa, yayin da jam’iyyar Republican ke fargabar yadda masu zaɓe za su mayar da martani a zaɓen da ke tafe.
Asali: Legit.ng

