2027: Uba Sani Ya Ari Bakin Gwamnonin Arewa Ya Ci Masu Albasa kan Shugaba Tinubu
- Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu 100%
- Gwamnonin sun bayyana cewa wajibi ne Arewa ta mutunta yarjejeniyar karba karba da ta yi da Kudu tun a shekarar 1999
- Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce yarjejeniyar ta tanadi cewa Arewa za ta yi wa’adi biyu a jere, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun sake tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu 100%.
Gwamnonin sun kuma jaddada cewa wajibi ne Arewa ta mutunta yarjejeniyar karba-karba na mulkin Najeriya da ta cimma da Kudancin Najeriya a 1999.

Source: Facebook
Vanguard ta ce Gwamna Uba Sani na Kaduna ne ya yi wannan jawabi a madadin dukkan gwamnonin Arewa yayin bikin ƙaddamar da sakatariyar ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) ta ƙasa da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
Wajen rantsar da kwamitin kamfe ya zama matattarar habaici tsakanin Akpabio, Wike da gwamnoni
"Ko ina, muna goyon bayan Shugaban Tarayyar Najeriya da 100% zuciyoyin mu," in ji shi.
Yarjejeniyar Arewa da Kudu
Da yake tuno yarjejeniyar da aka cimma a 1999, Gwamna Uba Sani ya ce Arewa da Kudu sun amince cewa Arewa za ta samu damar yin wa’adi biyu a jere a kan mulki.
Ya ce bisa wannan fahimta, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu, ya yi wa’adi biyu a jere, wato shekaru takwas a kan mulki.
Uba Sani ya bayyana cewa Kudancin Najeriya na da damar tsayar da ɗan takara ko ’yan takara, amma bai yi hakan ba saboda yarjejeniyar da aka cimma, musamman ganin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar.
Arewa za ta cika alkawari
Gwamnan ya amince cewa yarjejeniyar ba ta da wani tanadi a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, amma ya ce hakan bai kamata ya zama dalilin karya ta ba.
"Ba mu da wani dalilin da zai sa mu karya wannan alƙawari, duk da cewa ba ya cikin kundin tsarin mulki. Amma zan iya cewa akwai kundin tsarin mulkin hankali.
"Hankali ya nuna cewa dole ne mu mutunta wannan yarjejeniya ta fahimtar juna," in ji shi.
Gwamnonin Arewa sun goyi bayan Tinubu
Gwamna Sani ya shaida wa shugaban ƙasar cewa gwamnonin jihohin Arewa, waɗanda ya bayyana a matsayin ’yan dimokuraɗiyya da kuma ’yan kishin ƙasa, suna tare da shi.
Ya ce Shugaba Tinubu ya yi abin a yaba, kamar yadda shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana a jawabinsa.

Source: Twitter
Sani ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar da su fito fili su bayyana matsayarsu ba tare da tsoron faɗin gaskiya ba.
Abin da ya hana Tinubu nasara a Kaduna
Kun ji cewa mai magana da yawun APC a Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ya yi magana kan rashin nasara da Bola Tinubu ya yi a zaben 2023 a jihar.
Haruna ya danganta nasarar 'yan adawa a zaɓen 2023 da rashin gamsuwar jama'a da gwamnatin tsohon gwamna Nasir El-Rufai.
Ya ce salon mulkin Gwamna Uba Sani ya sauya siyasar Kaduna, inda ya haɗa mutane daga addinai, ƙabilu da jam'iyyun siyasa daban-daban.
Asali: Legit.ng
