Budurwa Ta Sallamawa Duniya Mahaifiyarta Bayan Ta Gano Tan Soyayya Da Saurayinta

Budurwa Ta Sallamawa Duniya Mahaifiyarta Bayan Ta Gano Tan Soyayya Da Saurayinta

  • Wata matashiya ta fito soshiyal midiya don nuna damuwarta bayan ta gano cewa uban ‘ya’yanta na soyayya da mahaifiyarta
  • Ta fara zargin akwai wata a kasa bayan ta gano cewa mutumin na kwana a gidan mahaifiyarta duk da cewar yana da nashi gidan da mota
  • Da ta tunkaresu a lokuta daban-daban, ya tabbatar da cewar suna soyayya, yayin da mahaifiyar bata musanta ba

Bayan ta gano cewa an yi wasa da hankalinta, wata matashiya ta saki hotunan hirarsu da uban 'ya'yanta da mahaifiyarta.

Matarshiyar mai suna @ChinChillaaaa_, ta bayyana a Twitter cewa ta gano saurayinta yana kwana a gidan mahaifiyarta harma yana da sifiyar makulen gidan.

Ta gano suna soyayya
Budurwa Ta Sallamawa Duniya Mahaifiyarta Bayan Ta Gano Tan Soyayya Da Saurayinta Hoto: PixelsEffect, Twitter/(@ChinChillaaaa_)
Asali: Twitter

A cewarta, hakan ya bata mamaki ganin cewa saurayin nata na da nashi gidan da mota.

Budurwar da ta karaya tace abu mafi muni shine cewa saurayin nata na kwana a gidan mahaifiyar tata ba tare da yaran suna nan ba.

Kara karanta wannan

Bayan Mijinta Ya Gaza a Gado, Wata Mata Ta Faɗi Yadda Ya Gwada Kwazon Direbanta Har Ya Mata Ciki Sau 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta tunkari masoyin nata wanda ba tare da nadama ba ya sanar da ita cewa soyayya suke yi.

Matashiya ta kuma tunkari mahaifiyarta kuma ita dinma bata musanta cewa akwai alaka kowani abu a tsakaninsu ba.

Daga hirarsu da ta yada, matashiyar ta kyamaci abun da mahaifiyarta ta aikata da kuma martaninta wanda sam babu nadama a ciki. Ta sallamawa duniya mahaifiyar tata.

"...Har muka gama musayar maganganu ita (mahaifiyar tata) bata musanta komai ba. Kawai tana ta kauce hanya ne da kokarin rufe zancen. Zuciyata na radadi kuma ba zan taba warkewa ba," ta koka a Twitter.

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@younggothamjedi ta ce:

“Idan wani gaye ya karya mani zuciya zan je na yi soyayya da mahaifinsa sannan ya zama dana.”
“Mata yan uwanki sun baiwa wannan mutumin irin wannan shawarar sai ya gudu da shi.”

Kara karanta wannan

Matashi Ya Halaka Mahaifin Budurwarsa Mai Shekaru 68 a Bauchi

@xoxosymoneb ta ce:

“Me yasa duk kuke dariya a wajen sharhi, babu abun dariya a nan. Shakka babu ta wallafa wannan ne saboda bata da wanda za ta fadawa yadda take ji ne. da ace ku ne da yanzu kun shirya yaki ko kasancewa a wani yanayi.”

@MiaaNoonan ta ce:

“Shin da ba zai dame ki ba idan kika ga mahaifinki yana soyayya da kakarki? Sannan zaki so ganin haka? Idan sauran yara suka gano sannan suka fara cin zarafin yaran fa? Idan yaran suka gano ko shakka babu zasu fahimci duk wata dangantaka a gaba ta baibai.

Bidiyo: Matashiya Yar Shekaru 40 Ta Koka Saboda Rashin Mijin Aure, Ta Roki Allah Ya Kawo Mata Agaji

A wani labarin, wata matashiyar budurwa mai shekaru 40 ta koka kan cewa bata jin dadin yadda abubuwa ke tafiya a rayuwarta.

Da take wallafa bidiyo a TikTok cike da rudani, budurwar ta rubuta cewa bata da haihuwa ko miji.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matashiya Yar Shekaru 40 Ta Koka Saboda Rashin Mijin Aure, Ta Roki Allah Ya Kawo Mata Agaji

Budurwar ta kara da cewa bata da wani tsayayyen namiji a yanzu haka sannan ta roki Allah da ya kawo mata dauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel