Yan Sanda Sun Kama Tunkiya Da Yaranta 2 Kan Cinyewa Dan Kasuwa Soyayyen Kifinsa

Yan Sanda Sun Kama Tunkiya Da Yaranta 2 Kan Cinyewa Dan Kasuwa Soyayyen Kifinsa

  • Yan sanda a jihar Borno sun kama wata tunkiya da yaranta biyu sakamakon barna da ta yiwa wani tireda
  • Yusuf Ibrahim ya yi karar tumakin ofishin yan sanda bayan ta cinye masa tulin soyayyen kifi da ya kasa yana siyarwa lamarin da ya sanya shi asara
  • Mai tumakin, Luba Mohammed ta baiwa Ibrahim hakuri inda ta yi alkawarin siyar da su ta huta ko kuma ta daure su a gida

Borno - Rundunar yan sandan Borno ta kama wata tunkiya da yaranta biyu kan cinye tulin soyayyen kifi da wani ya baza yana tallatawa a unguwar Vulabulin da ke Maiduguri, babban birnin jihar, shafin Zagazola ya rahoto.

An kama tumakin ne bayan wani tireda mai suna Yusuf Ibrahim wanda ke siyar da kifi a yankin ya shigar da kara.

Kara karanta wannan

Tsaiko ga daliban Najeriya yayin da ASUU ke shirin komawa yajin aiki saboda dalili 1

Jami'an yan sanda
Yan Sanda Sun Kama Wasu Tinkiyoyi Kan Cinyewa Dan Kasuwa Soyayyen Kifinsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya yi korafin cewa wannan tunkiya da ake magana a kanta ta shafe tsawon shekaru tana addabarsa ta hanyar yin yar buya tsakaninta da shi da kuma kayan sana’arsa.

A cewarsa, tunkiyar ta kan jira wani abu ya janye mai hankali sannan sai ta gaggauta cika baki da kifin har sai shi ko wasu sun Ankara sannan a fatattake ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce ya shafe tsawon shekaru yana hakuri da wannan hali na tunkiyar amma abun ya kai masa bango a ranar Asabar domin ta’asar da tayi masa ya sa shi asarar kudi ba kadan ba.

Luba Mohammed, mamallakiyar tumakin, ta ce ta shiga rudani lokacin da tumakin nata suka fara kwadaituwa da soyayyen kifi.

Ta ce Ibrahim ya kai mata korafin abun da tunkiyar ke masa amma ta roke shi da yayi hakuri.

Kara karanta wannan

Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta

Luba ta ce zata dauki tsattsauran mataki a kan tumakin nata ta hanyar siyarwa, yankata ko kuma daure su a gida.

An tattaro cewa lamarin ya kai har dare domin Luba, Ibrahim da dattawan da suka nuna kula sun tattauna yadda za a magance lamarin a ofishin yan sanda.

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Borno, Kamiludeen Sabi ba, rahoton TheCable.

Budurwa Ta Baro Dubai Zuwa Najeriya Saboda Bikin Kawarta, Ta Gano Ashe Saurayinta Zata Aura

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya wacce ta yo tattaki daga kasar Dubai ta gano cewa aminiyarta tayi mata kwacen saurayi.

A bisa ga wani bidiyo da ta wallafa a TikTok a ranar Juma'a, 4 ga watan Nuwamva, aminiyarta zata yi aure sai ta ganke shawarar halartan baikonta.

Amma ga mamakinta, Princess tace da ta isa wajen bikin baikon, sai ta gano cewa mijin saurayinta ne.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya fadi wadanda zai siyarwa matatun man Najeriya idan ya gaji Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel