Budurwa Ta Baro Dubai Zuwa Najeriya Saboda Bikin Kawarta, Ta Gano Ashe Saurayinta Zata Aura

Budurwa Ta Baro Dubai Zuwa Najeriya Saboda Bikin Kawarta, Ta Gano Ashe Saurayinta Zata Aura

  • Wata budurwa yar Najeriya da ta hadu da sharrin soyayya ta je TikTok ta bayyana yadda aminiyarta ta kwace mata saurayi yayin da take Dubai
  • Budurwar mai suna Princess Toria ta bayyana a wani gajeren bidiyo cewa ta gano aminiyarta zata amarce da saurayinta
  • A cewar Princess, ta shigo Najeriya ba tare da sanin kowa ba don ba aminiyarta mamaki, amma sai daga bisani ta bankado lamarin mai ban al'ajabi

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya wacce ta yo tattaki daga kasar Dubai ta gano cewa aminiyarta tayi mata kwacen saurayi.

A bisa ga wani bidiyo da ta wallafa a TikTok a ranar Juma'a, 4 ga watan Nuwamva, aminiyarta zata yi aure sai ta ganke shawarar halartan baikonta.

Toria
Princess Toria ta ce aminiyarta zata amarce da saurayinta Hoto: TikTok/@princess_toria23.
Asali: UGC

Amma ga mamakinta, Princess tace da ta isa wajen bikin baikon, sai ta gano cewa mijin saurayinta ne.

Kara karanta wannan

Kebera yake sha? Bidiyon mataccen takalmin da wani ya saka ya je neman aure ya ba mamaki

Ta ci gaba da cewar aminiyar tata har ta haifawa saurayin nata yaro dan shekaru biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Labarin ya kada hantar cikin mutane da dama domin abun akwau al'ajabi, inda wasu suka kira ta da makaryaciya.

Princess ta wallafa bidiyon lokacin da take barin filin jirgin sama zuwa Najeriya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@King IBM ya ce:

"Mai shayar da mamaki an shayar da ita mamaki.. wow, yarinya mai mamaki."

@Pearl Essentials ta yi martani:

"Kun cika karya a manhajar nan."

@Cherish29 ta ce:

"Wato bata yi hoto da saurayinta ba tun lokacin kuma baki tambayeta hotunanda da angon nata ba?"

@__onlyonethiffy$ ta ce"

"Kana kokarin ba wani mamaki sai a karshe kai aka shayar da kai mamaki. Wow! Karayar zuciya."

@bannyella ta rubuta:

Kara karanta wannan

Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta

"Wai zolayata kike yi ne."

@Canada Lucas ya ce:

"Ba kawar bace idan baki san angonta ba."

Mace Ba Yar Goyo Bace: Bakano Ya Je Shagalin Auren Aminsa, Ya Gano Budurwarsa Ce Amaryar

A wani labarin, wani matashi dan Najeriya ya shawarci masu amfani da shafukan soshiyal midiya da kada su taba yarda da mace yayin da ya bayyana yadda budurwa tayi rugu-rugu da zuciyar abokinsa.

Sambo Mai Hula ta shafinsa na twitter mai suna @Abdullahiabba_ ya bayyana cewa abokinsa ya halarci shagalin bikin auren wani aminsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba.

Ga mamakin abokin Sambo, sai yaga cewa amaryar ba kowa bace face wata budurwa mai suna Fatima wacce ya shafe tsawon shekaru uku suna soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel