Dalibar Likitanci ta Fara Sana’ar Gwanjo da N2k, Tayi Arzikin N48.5m Har da Siyan Gida

Dalibar Likitanci ta Fara Sana’ar Gwanjo da N2k, Tayi Arzikin N48.5m Har da Siyan Gida

  • Wata budurwa mai shekaru 26 dake fama da matsanancin bashi ta samu mafita bayan ta fada sana’ar siyar da gwanjo kuma take cake ‘yan sulallarta
  • Olivia Hillier tace ta siyo riga guda daya kan N2,000 kuma ta siyar da ita kan N8,000 kuma hakan ya kawo tushen kasuwancin ta da yayi kamari yanzu
  • Kamar yadda tace, jimillar ribar da ta samu a kasuwancinta ya kai sama da N48 miliyan kuma ta siya katafaren gida mai dakuna biyar reras

Olivia Hillier ta fara kasuwancinta da $5 kadai wanda yayi daidai da N2,000 inda ta siya riga daga shagon gwanjo kuma ta siyar.

Olivia mai gwanjo
Dalibar Likitanci ta Fara Sana’ar Gwanjo da N2k, Tayi Arzikin N48.5m Har da Siyan Gida. Hoto daga Olivia Hillier
Asali: UGC

Daliba mai karatun likitancin a Rochester, wata jami’a dake Michigan mai suna Oakland University kuma ta samu gogewa tun farko ta hanyar siyar da wasu daga cikin tsofaffin kayanta a manhajar Poshmark. Duk da bata mayar da hankali sosai a kai ba.

Kara karanta wannan

Waye Mahaifin ki a Najeriya? ‘Yar TikTok Mai Shekaru 17 ta Siya Motar N20m

Amma annobar korona ta taso a 2020 kuma Hillier ta gane cewa sauran masu siyar da kayayyaki a Poshmark suna samun riba ta hanyar siyar da gwanjo.

Tsabar bashi ya dameta

Sakamakon bashin da ake bin ta da ya addabeta da kuma kudin makarantarta da ya kai $220,000 na shekaru hudu, Hillier ta fara karantar tsarin mutane kuma ta fara kirkirar sana’ar da zata yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rigar farko da ta siyo kan N2,000 ta siyar da ita kan N8,000. Daga nan Hillier ta cigaba da sana’a kuma ta hada N48.5 miliyan jimillar riba har da N35.2 miliyan a shekarar da ta gabata kadai.

Tana samun kudi kowanne wata

Kasuwancinta a halin yanzu yana samar mata da N2.5 miliyan zuwa N2.9 miliyan na riba kowanne wata kamar yadda CNBC ta bayyana.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Yadda budurwa ta haifi jaririnta a jirgin sama mai nisan kafa 36,000 a sama

Kasuwancin ya taimaka mata wurin samun kudin adanawa kuma bata karbar bashi domin samun yin lamurran rayuwarta.

Tsarin kasuwancinta

Tace ta raini kasuwancinta ta hanyar bincike a watan Augustan 2020 kuma ta gane cewa wasu masu siyar da kayayyaki a Poshmark suna saka dubban abubuwan siyarwa da ba dole a samu a akwatinan su ba. Daga nan ta gane cewa daga wurin masu gwanjo suke samowa.

Kamar yadda tace, ta fara karantar yadda tsarikan wasu masu irin kasuwancin suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel