Ina Nan a Raye' Tsohon Ministan Buhari Ya Yi Watsi da Rahoton Cewa Ya Mutu a Bidiyo

Ina Nan a Raye' Tsohon Ministan Buhari Ya Yi Watsi da Rahoton Cewa Ya Mutu a Bidiyo

  • Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya yi martani a kan jita-jitan da ke yawo na cewa ya kwanta dama
  • Dalung wanda ya riki mukamin minista a wa'adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na farko ya ce yana nan da ransa kuma cikin koshin lafiya
  • Mabiya shafinsa na soshiyal midiya sun yi masa fatan alkhairi tare da yi masa ta'aziyyar rashin da yayi a kwanan baya

Tsohon ministan wasanni da ci gaban matasa, Solomon Dalung, ya yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa ya mutu.

A kwanaki ne Dalung, wanda ya kasance ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2019, ya rasa dansa mai suna Nehemiah inda shi da kansa ya fito ya sanar da labarin.

Tsohon minista
Ina Nan a Raye' Tsohon Ministan Buhari Ya Yi Watsi da Rahoton Cewa Ya Mutu a Bidiyo Hoto: Barrister Solomon Dalung
Asali: Facebook

Tsohon ministan wanda ya jadadda cewa yana nan da ransa ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sarkin Shagamu Ya Makantar Da Ni Saboda Na Yi Rawa Da Matarsa, Mai Abinci

Ya rubuta a jikin bidiyon nasa cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina nan da raina, cikin koshin lafiya da karfin zuciya, dan Allah kuyi watsi da rade-radin mutuwata. Allah ya albarkaci Najeriya.”

Yan Najeriya da dama sun yi martani inda wasu suka yi amfani da wannan damar wajen mika ta'aziyyarsu gare shi a kan rashin dansa da yayi kwanaki.

Nuhu Yaro ya ce:

"Ajiyan Allah sai Allah....!"

Aliyu Magayaki Kiru ya ce:

"Ka yi hakuri Hon Minista. Allah ya sanyaya zuciyarka."

Nanzing Zwal ya yi martani:

"Wannan jita-jitan ne mai muni, Kai Dan Najeriya. Koma wanene ya yada wannan labarin. Godiya ga Allah tunda kana raye abokina."

Emmanuel Nwoba ya ce:

"Za ka ci gaba da rayuwa."

Hon Speaker Kalamullah ya ce:

"Yallabai na kira daren jiya ba a amsa ba da fatan kana lafiya."

Vongjen Patience Nanfe ta ce:

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Rubutu daya a Twitter ya jawo wani matashi ya gaza samun aiki a banki

"Ka dauki dangana, na ga alama har yanzu kana cikin alhinin rashi."

Isaac Okubor Brenda ya yi martani:

"Dan Allah ka karbi ta'aziyyata yallabai, ba zan iya cewa na san yadda kake ji ba ko yadda ka ji tsawon wasu kwanaki yanzu ba amma ina mai tausaya maka sosai yallabai.]

Ado Bala ya ce:

"Barka da safiya yallabai. Ya karin hakurinmu."

Abu Magaji Tsafe ya ce:

"Ina maka fatan tsawon raki cikin arziki da koshin lafiya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel