Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Mazge Matar Aure Har Cikinta Ya Zube

Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Mazge Matar Aure Har Cikinta Ya Zube

  • Babbar kotun yanki dake zama a Karu babban birnin tarayya, ta gurfanar da wani matashi kan zargin mazgar wata mata har cikinta ya zube
  • Mai gabatar da kara yace a watan Satumba Okechukwu Eze mai shekaru 37 ya make Anthonia a ciki a tashar Nyanya duk don hana ta shiga motar wani direba
  • Alkali ya bayar da belin Eze kan N100,000 tare da tsayayye daya wanda ake zama a yankin da kotun ke da iko sannan yasa hannu kan gujewa tada tarzoma

Osun - Wata babbar kotun yanki dake Karu a Abuja ta gurfanar da wani Okechukwu Eze mai shekaru 37 kan zargin cin zarafin wata mata tare da janyo zubewar cikinta.

Gudumar Kotu
Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Mazge Matar Aure Har Cikinta Ya Zube. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: Facebook

’Yan saNDA sun gurfanar da Eze sakamakon laifin da ake zarginsa wanda har ya kai ga barewar cikin wata mata kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Lauyan masu gurfanarwa mai suna Olanrewaju Osho ya sanar da kotun cewa, a watan Satumba karkashin tashar Nyanya dake Karu, wanda aka gurfanar ya ci zarafin mai korafi inda ya duketa a ciki a kokarinsa na hana direba daukanta.

Osho yace wacce ke korafin mai suna Anakputa Anthonia wacce ke zaman a Gogo Close kusa da hedkwatar NSCDC dake Kubwa, ta zargi cewa wannan lamarin ne ya janyo mata zubewar ciki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Laifin yace ya ci karo da tanadin sashi na 365 na kundun Penal Code.

Wanda ake zargin ya musanta aikata abinda ake zarginsa da shi.

Alkali Hassan Muhammad ya bayar da belin wanda ake zargi kan N100,000 tare da tsayayye daya wanda ke zama a inda kotun ke da hurumin shari’a.

Mohammed yayi umarnin cewa dole ne kotu ta tantance adireshin wanda ya tsaya masa tare da ‘dan sanda, a ajiye katin ‘dan kasa da fasfoti daya a gaban kotun.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas

Alkalin yayi umarnin cewa wanda ake zargin ya je ya rubuta takarda ta tabbacin cewa ba zai sake tayar da tarzoma ba.

Mohammed ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba mai zuwa.

A Raba Ni Da Matata Kafin Hawan Jini Yayi Ajalina, Magidanci ga Alkali

A wani labari na daban, wani miji mazaunin gida mai suna Gyang Gyang ya maka matarsa mai suna Jemima a gaban wata kotun gargajiya dake Nyanya kan cewa bata masa biyayya kuma tana fita babu izininsa.

Mai karar ya bayyana wannan zargin ne a bukatar sakin da ya mika a gaban kotun, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel