Wata Sabuwa: Twitter Zata Kallafa Harajin N16,000 Kan Masu Asusun da Kaa Tantance

Wata Sabuwa: Twitter Zata Kallafa Harajin N16,000 Kan Masu Asusun da Kaa Tantance

  • Hamshakin attajiri Elon Musk da ya siya kamfanin Twitter zai kallafa harajin N16,000 kan duk masu asusun da aka tantance a kafar sada zumuntar zamanin
  • Kamar yadda Verge ta bayyana, duk wanda bai biya N16,000 a kowanne wata ba zai rasa alamar tantancewarsa na asusun Twitter din shi
  • Har ila Yau, Musk ya bai wa ’yan tawagar aikin kallafa harajin zuwa 7 ga watan Nuwamba da su kammala ko ya koresu daga aiki

Amurka - An gano cewa, kafar sada zumuntar zamani ta Twitter tana da niyyar kallafawa jama’a harajin $20 amma ga duk masu asusun da aka tantance.

Twitter
Wata Sabuwa: Twitter Zata Kallafa Harajin N16,000 Kan Masu Asusun da Kaa Tantance. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Fitaccen biloniya kuma mamallakin Tesla, Elon Musk, wanda cikin kwanakin nan ya mallaki kafar sada zumuntar zamanin yana aiki kan manyan canje-canje tare da kokarin ganin ya samu zunzurutun riba daga hannun jarinsa.

Kara karanta wannan

Zargin Damfara: ‘Dan Takarar Sanatan APC a Kano Ya Ki Bayyana Gaban Kotu, EFCC

Wani rahoto da Verge suka fitar ya bayyana cewa Twitter na kokarin ganin ta kara kudin masu tantantaccen asusu daga $4.99 zuwa $19.99 a kowanne wata ko kuma mutum ya rasa tantancewarsa.

An rahoto cewa, dole ne wadanda ke da tantantaccen asusun su bi wannan sabuwar dokar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani editan Verge mai suna @Alex Heath wanda ya bayyana labarin nan yace sabuwar dokar zata fara aiki ne a ranar 7 ga Nuwamba kuma idan tawagar dake aikin ba su kaddamar da sabuwar dokar ba za a kore su daga aiki.

Yace:

“Labari: Twitter na shirin fara karbar $20 na tantancewa a kowanne wata. Wannan shi ne aikin Elon Musk ba farko.
“Toh ga tawagar dake aikin, an sanar cewa za a kore su idan basu kaddamar da shi ba zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba.”

Kara karanta wannan

Fargabar Hari: Bayan Jabi Lake Mall, Wani Babban Kamfani Ya Sake Rufe Ayyukansa A Abuja

Rahoton ya kara da bayyana cewa, masu tantantaccen asusu za a basu kwana 90 su koma Twitter Blue ko kuma su rasa alamar tantancewarsu.

An kara da bayyana cewa, ba fitattun mutane da jarumai ne kadai zasu samu alamar tantancewar ba, har da ma’abota amfani da Twitter din da aka tabbatar da su din ne za a tantance.

A ranar Juma’a, 28 ga watan Oktoba ne hams hamshakin mai kudin ya mallaki kafar sada zumuntar zamanin.

Elon Musk Ya Kori Shugaban Tuwita Da Wasu Manyan Shugabanni 2 - Awanni Bayan Ya Siya Kamfanin

A wani labari na daban, Elon Musk, biloniya kuma wanda ya kafa kamfanin Tesla Inc., ya sallami manyan shugabannin Twitter, The Cable ta rahoto.

Hakan na zuwa ne kasa da kwana guda bayan ya kammala cinikin siyan Tuwita, kuma bayan Musk ya yi alkawarin ba zai kori ma'aikata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel