Hotuna da Bidiyoyin: Otedola Yayi Shatar Jirgin Ruwa da N1.4b don Shagalin Bazdensa

Hotuna da Bidiyoyin: Otedola Yayi Shatar Jirgin Ruwa da N1.4b don Shagalin Bazdensa

  • Hamshakin ‘dan kasuwar nan fetur, Femi Otedola, zai kashe N1.4 biliyan wurin hayar jirgin ruwan da za a yi shagalin zagayowar ranar haihuwarsa karo na 60
  • Otedola tare da iyalansa da abokan arziki zasu kwashe makonni uku a cikin jirgin ruwan yana yawo da su tare da ma’aikata 38 ciki har da masu tausa
  • Jirgin ruwan mai suna Christina O mallakin marigayin hamshakin mai arzikin duniya ne, Aristotle Onassis kuma an ga Otedola tare da iyalansa suna duba shi

Fitaccen attajirin ‘dan kasuwar Najeriya, Femi Otedola, ya fitar da zunzurutun kudi har N1.4 biliyan inda yayi hayar katafaren jirgin ruwa.

Femi Otedola
Hotuna da Bidiyoyin: Otedola Yayi Shatar Jirgin Ruwa da N1.4b don Shagalin Bazdensa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

‘Dan kasuwar man wanda zai cika shekaru 60 a duniya a ranar 4 ga watan Nuwamba, ya yanke shawarar yin wannan shagalin cikin kawa da kashe kudi.

A wani bidiyo da ya yadu, an ga Otedola da iyalansa tare da sirikinsa Mista Eazi suna gaisawa da matukan katafaren jirgin ruwan na alfarma wanda ake kira da Christiana O, mallakin Aristotle Onassis.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Kamar yadda rahotanni suka bayyana daga @fashionseriesng, jirgin ruwan zai kwashe makonni uku yana yawo da biloniyan tare da iyalansa da abokan arziki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gagarumin jirgin ruwan wanda ya kasance wanda yafi kowanne jirgin ruwa girma a duniya, mallakin abokin Otedola ne na yarinta, marigayin hamshakin mai arziki Aristotle Onassis wanda ya taba kasancewa mutumin da yafi kowa kudi a duniya.

Otedola yana daya daga cikin attajiran Najeriya wanda kudinsa ya samu ne ta hanyar shigo da man fetur. Shi ne kuma ya mallaki Zenon Petroleum and Gas Ltd, kuma ya mallaki wasu kasuwancin a fannin jiragen ruwa, gidaje da hada-hadar kudi.

Kamar yadda bayanin yanar gizo ya bayyana, a watan Janairun 2022, ana shatar wannan jirgin ruwan kan N470 miliyan a kowanne mako daya har da kudin haraji.

Akwai ma’aikata 38 a ciki wadanda suka hada da masu tausa guda biyu. Jirgin ruwan ya karba bakuncin manyan shugabannin kasashen duniya da ministoci kamar su John Kennedy da Sir Winstonw Churchill tare da sannanun mutane irinsu Marilyn Monroe da Frank Sinatra.

Kara karanta wannan

Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima

Hotunan Seyi Tinubu yana zantawa da Dangote, Osinbajo da Obasanjo a bazden mahaifiyar Otedola

A wani labari na daban, Asiwaju Bola Tinubu, Jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa kuma dan takarar shugabancin kasa a shekarar 2023, bai samu hallartar shagalin bikin zagaoyowar ranar haihuwar mahaifiyar fitaccen biloniya Femi Otedola ba da aka yi a Epe dake jihar Legas.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo; tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki; Attajirin Afrika, Aliko Dangote, suna cikin manyan baki da suka halarci taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel