Kwana Ya Kare: Tsohon Hadimin Shugaban Kasa a Najeriya Ya Rasu
- Fitaccen ɗan jarida kuma tsohon jakadan Najeriya, Dele Cole, ya riga mu gidan gskiya yana da shekaru 86 a duniya
- Marigayin ya taɓa zama manajan daraktan jaridar Daily Times kafin naɗa shi jakadan Najeriya a kasashen Argentina da Brazil
- Ya taɓa zama mai ba Shugaba Olusegun Obasanjo shawara kan harkokinnhulɗar ƙasashen duniya daga shekarar 1999 zuwa 2007
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Tsohon hadimin shugaban kasa kuma tsohon jakadan Najeriya a kasashen waje, Ambasada Dele Cole, ya riga mu gidan gaskiya.
Majiyoyi daga iyalan fitacccen dan jaridan sun tabbatar da cewa ya rasu da safiyar yau Asabar, 17 ga watan Oktoba, 2026 yana da shekaru 86 a duniya.

Source: Facebook
Marigayin ya taɓa zama manajan daraktan jaridar Daily Times kafin daga bisani aka naɗa shi jakadan Najeriya a ƙasashen Argentina da Brazil.
Abubuwan sani game da Cole
An haifi Ambasada Cole a ranar 4 ga Agusta, 1940, a Abonnema, da ke masarautar Kalabari a jihar Rivers ta yanzu.
Ya fara karatunsa a makarantar St Bartholomew’s da ke Enugu, inda ya yi karatu daga shekarar 1946 zuwa 1953.
Daga nan Cole ya halarci makarantar Baptist High School da ke Fatakwal daga 1954 zuwa 1958, sannan ya wuce Ibadan Grammar School, inda ya yi karatu daga 1959 zuwa 1960.
A shekarar 1962, ya bar Najeriya zuwa ƙasar New Zealand domin neman ilimi a matakin gaba a Jami’ar Otago da ke Dunedin, inda ya yi karatu har zuwa shekarar 1965.
Daga baya, Dele ya halarci Jami’ar Cambridge daga 1966 zuwa 1970. Ya kuma yi karatu a Kwalejin King’s da ke Cambridge, inda ya kasance ɗan ƙungiyar malamai daga 1970 zuwa 1973, tare da samun digirin digirgir (PhD) a fannin tarihi.
Mukaman da Dele Cole ya rike
A shekarar 1975, aka naɗa shi daraktan da ba ya gudanar da ayyukan yau da kullum a jaridar Daily Times.
Daga 1999 zuwa 2007, ya yi aiki a matsayin mai ba Shugaba Najeriya na wancan lokacin, Olusegun Obasanjo shawara na musamman kan hulɗar ƙasashen duniya.
Haka kuma, an naɗa shi jakadan Najeriya a ƙasashen Brazil da Argentina, inda ya yi aiki a matsayin jami'in diflomasiyya.
Deleke Cole ya kuma shiga harkokin siyasa, inda ya yi hulɗa da jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a shekarun 1990.
Tsohon shugaban FRSC ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da rasuwar tsohon shugabanta, Dauda Ali Biu, inda ta bayyana matukar kaduwarta kan wannan babban rashi.
FRSC ta bayyana marigayin a matsayin jami’i mai kishin aiki da ladabi wanda ya bayar da gagarumar gudummawa wajen gudanar da harkokin kiyaye lafiyar masu amfani da hanya da kuma ci gaban hukumar.
Dauda Biu, wanda ya shiga FRSC a shekarun farko na kafuwar hukumar, ya samu karin girma zuwa matakai daban-daban har ya zama shugaban hukumar na bakwai a tarihi.
Asali: Legit.ng

