Tashin Hankali: Yan Daba Dauke da Makamai Sun Kewaye Jigon APC, Sun Kashe Shi Nan Take
- An kashe wani mamba a jam’iyyar APC mai suna Ridwan Adeyemo a Ibadan, jihar Oyo, bayan wasu da ake zargin yan daba ne sun far masa da makamai
- Jam’iyyar APC a jihar Oyo ta tabbatar da kisan, inda ta yi kira ga ’yan sanda da su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin
- Jam’iyyar ta yi zargin cewa an kashe Adeyemo ne saboda kasancewarsa mai goyon bayan APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun kashe wani mamba a jam’iyyar APC, Ridwan Adeyemo, a ranar Juma’a a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
An ce an kashe Adeyemo ne a yankin Agbokojo, da ke ƙaramar hukumar Ibadan ta Arewa maso Yamma a jihar.

Source: Getty Images
Tribune Nigeria ta ce rahotanni sun bayyana cewa maharan sun far wa Adeyemo da muggan makamai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Sai dai da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ayanlade Olayinka, ya ce ba zai iya tabbatar da harin ba.
Amma jam’iyyar APC ta jihar Oyo ya tabbatar da kisan a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta, Olawale Sadare, ya fitar, inda ya yi kira ga ’yan sanda da su binciki lamarin.
Sanarwar ta ce Adeyemo ɗan APC ne a mazaba ta 06 da ke ƙaramar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma, kuma yana sana’ar tuƙa babur na haya.
An kashe shi ne a wurin da yan daban suka rutsa shi, a yankin Ita-Barika da ke Agbokojo, Ibadan, inda rahotanni suka ce wasu gungun mutane masu ɗauke da makamai suka far masa.
APC ta yi Allah wadai da kisan
Shugabannin jam’iyyar a jihar, ƙarƙashin jagorancin Sakataren jam’iyyar na jihar, Hon. Fatai Adesina, sun yi Allah wadai da kisan yayin ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Adesina ya bayyana lamarin a matsayin harin da aka kai da tsakar rana, wanda ya jefa al’umma cikin firgici da tashin hankali.
Ya ce:
"Mun samu labarin wannan mummunan aika-aika cikin daren Juma’a, abin da ya girgiza mu matuƙa.
“Abin ya ƙara tayar mana da hankali shi ne da muka gano cewa an far wa marigayin tare da kashe shi saboda kasancewarsa mai biyayya ga APC domin kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, waɗanda suka kashe shi sun tambaye shi dalilin da ya sa ya zaɓi zama a APC maimakon sauran jam'iyyu.
“Muna da wasu bayanai da za su iya taimaka wajen gano waɗanda suka kai harin da kuma dalilan da suka sa suka aikata wannan mummunan kisan, amma za mu riƙe su a yanzu domin kada mu kawo cikas ga binciken ’yan sanda."

Source: Original
Yan daba sun farmaki yan PDP
Kun ji cewa jam’iyyar PDP a Jihar Cross River ta yi zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hare-haren bindiga kan tarukan da ta shirya a Ƙaramar Hukumar Calabar South.
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP a jihar, Mike Ojisi, ya bayyana abubuwan da suka faru a matsayin “hare-hare masu tayar da hankali” kan tarukan tuntubar jama’a na jam’iyyar.
Asali: Legit.ng

