Yadda Uwa Ta Sayar da Jaririyarta Naira Miliyan 2 Wata 1 bayan Haihuwa

Yadda Uwa Ta Sayar da Jaririyarta Naira Miliyan 2 Wata 1 bayan Haihuwa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta ceto wata jaririya da aka sayar kan naira miliyan biyu sannan ta kama mutum biyu da ake zargi
  • Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Ido da ke Ibadan, inda 'yan sanda suka tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran mutane
  • Jami'in Yaɗa Labarai na Rundunar 'Yan Sandan, DSP Olayinka Ayanlade, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ibadan – Rundunar 'yan sandan Jihar Oyo ta yi nasarar ceto wata jaririya yar wata ɗaya kacal wadda aka sayar kan kuɗi naira miliyan 2, tare da kamas mahaifiyarta da kuma mai gidan cibiyar lafiyar da aka haife ta.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da tsagerun 'yan bindiga, an ceto mata bayan zubar da jini

Rundunar ta bayyana cewa an gudanar da wannan ɗanyen aiki ne a yankin Ido na birnin Ibadan, sannan ana ci gaba da neman sauran waɗanda ke da hannu a cikin batun cinikayyar yaran.

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa an shigar da ƙarar lamarin ne a ranar 15 ga watan Oktoba ta hannun Mary Amos, wata mazauniya yankin Ogunwade da ke Ido, wadda ta nuna damuwa kan ɓacewar jikarta.

An sayar da jaririya a Oyo

Rundunar 'yan sanda ta ce mahaifiyar jaririyar, wadda aka gano sunanta da Cecilia, ta fallasa mai cibiyar lafiyar, ɗan shekara 40, da wani mutum daban, inda ta yi zargin cewa su ne suka yaudare ta har aka sayar da jaririyar ga wani mai suna Odunayo.

Bincike ya nuna cewa an gudanar da cinikayyar ne a kan naira miliyan 2, inda aka bai wa Cecilia naira miliyan 1, yayin da sauran mutane biyun suka raba N500,000 kowannensu.

Ta bayyana cewa:

"'Yan sanda sun sami nasarar ceto jaririyar tare da kama Adeleke, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama Folawewo domin gurfanar da sauran waɗanda ke da hannu a cikin lamarin gaban shari'a."

Kara karanta wannan

Samaila Kaigama ya fara fuskantar hukunci kan zargin taimaka wa 'yan ta'adda a Najeriya

Taswirar jihar Oyo
Taswirar jihar Oyo a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Alƙawarin rundunar 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan ta sake jaddada aniyarta na kare haƙƙin yara da sauran mutane masu rauni a cikin al'umma.

A cewar jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, ana ƙarfafa gwiwar al'umma wajen kai rahoton duk wani abin zargi da ya shafi fataucin yara da sauran laifi ba tare da ɓata lokaci ba.

"Rundunar 'yan sandan Jihar Oyo tana sake jaddada aniyarta na kare yara da mutane masu rauni, kuma tana buƙatar al'umma da su gaggauta kai rahoton duk wani zargi na fataucin yara da laifuka masu alaƙa."

EFCC ta cafke dan Shehin Darika

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar EFCC ta gurfanar da wani mutum mai suna Abdulmajid Halifa Nazifi a gaban Kotun Ƙoli ta Jihar Kano kan zargin karkatar da naira miliyan 34.875 da aka ba shi domin sayen taliyar BUA.

An gurfanar da Nazifi ne a ranar Laraba a gaban Mai Shari'a Musa Karaye kan tuhuma guda ɗaya ta karkatar da dukiyar jama'a ta hanyar ha'inci.

A cewar tuhumar, wanda ake zargin ya karkatar da kuɗi mallakar Fahad Balarabe Adaji ne tsakanin Satumba da Oktoba na shekarar 2024 a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng