Buhari Ya So Osinbajo Ya Zama Shugaban Kasa, Hadimi Ya Karyata Babachir Lawal

Buhari Ya So Osinbajo Ya Zama Shugaban Kasa, Hadimi Ya Karyata Babachir Lawal

  • Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa ya karyata Babachir Lawal da ya ce Muhammadu Buhari bai tare da takararsa
  • Laolu Akande ya ce mairgayi tsohon shugaban na Najeriya da kansa ya nuna zai tallafa wa takarar Yemi Osinbajo sau da dama
  • Ya kuma ce tawagar Farfesa Osinbajo ta kunshi mutane masu nagarta daga sassa daban-daban, ba ‘yan cocinsa na RCCG kawai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya shiga zancen da aka tado da shi.

Babachir David Lawal ya yi ikirarin marigayi Muhammadu Buhari bai goyi bayan Yemi Osinbajo ya zama shugaban Najeriya ba.

Buhari-Yemi Osinbajo
Marigayi Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo lokacin kamfe a 2015 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hadimin Yemi Osinbajo ya fitar da jawabi a X

A shafinsa na X, Laolu Akande, ya ce marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna zai goyi bayan Farfesa Osinbajo.

Kara karanta wannan

An gano babban dalilin Buhari na kin amincewa Osinbajo ya fafata da Tinubu a 2023

Marubucin ya ce marigayin ya nuna zai mara wa Osinbajo baya a neman takararsa ta shugaban kasa a karkashin APC akalla sau hudu.

‘Dan jaridan ya ce aikinsa a ofishin mataimakin shugaban kasa ya ba shi damar sanin dangantakar da ke tsakanin Buhari da Osinbajo.

Laolu Akande ya karyata Babachir Lawal

Akande ya bayyana hakan ne domin karyata ikirarin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, wanda ya koma NDC.

Babachir ya fito yana cewa Buhari ya dauki matakin Osinbajo na shiga takara da mai gidansa, Bola Tinubu a matsayin rashin biyayya.

Injiniya Babachir ya ce shugaba Buhari ya dauki biyayya da muhimmanci sosai don haka, bai ji dadin ganin Osinbajo zai yaki Tinubu ba.

Buhari ya goyi bayan takarar Osinbajo a APC?

A cewar Akande, Buhari ya karfafa wa Osinbajo gwiwa kan burinsa na zama shugaban kasa da ya fito neman tikitin APC a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Ana zargin Kwankwaso na taimakon Tinubu ya zarce sabdao wasu dalilai

Fasto Akande ya ce marigayin ya kuma yaba masa a bainar jama'a kan yadda ya gudanar da kamfen dinsa na neman tikitin jam’iyya.

Sai dai Akande ya ce kalamai da ayyukan Buhari sun saba da maganganun Babachir.

Lokutan da Buhari ya nuna wa Osinbajo goyon baya

Tsohon hadimin ya fitar da sanarwa a ranar Asabar mai taken “Martani ga karyace-karyacen Babachir Lawal kan Farfesa Yemi Osinbajo”

Akande ya ce Buhari ya taba gaya wa Osinbajo cewa: “Idan ba zan goyi bayanka ba, wa zan goya wa baya?”

Sannan ya kuma tuna cewa a shekarar 2022, lokacin da ake fafatawa domin samun tikitin, Buhari ya yaba wa Osinbajo wajen taron FEC.

A rubutun, ya ce kalaman Buhari sun nuna cewa bai adawa da burin Osinbajo na zama shugaban kasa ba bayan wa’adinsa ya kare.

Maimakon haka, ya ce ya tattauna batun, ya karfafa masa gwiwa, sannan ya yaba masa.

Kakaki ya ba tsohon mataimakin shugaban kasa kariya

Haka kuma, Akande ya karyata wani zargi na daban da Lawal ya yi cewa an yi la'akari da kabila da addini wajen nada ‘yan kamfen.

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

A raddin nasa, ya nuna yadda Osinbajo ya yi aiki da mutane daga ko ina a Najeriya, ya ce babban jami’i a ofishinsa, Ade Ipaye, musulmi ne.

Cikin manyan hadimai kuwa, ya ce Mrs. Maryam Uwais, Dr. Ahmad Zakari da Babafemi Ojudu ba kiristoci ba ne kamar yadda ake riyawa.

Rubutun ya kawo zancen Dr. Okey Enelamah, aka karyata cewa ya zama minista ne saboda kasancewarsa fasto a cocin su Osinbajo.

Ya kare da cewa Osinbajo ya yi wa Buhari biyayya tsawon shekaru takwas da suka yi tare a gwamnati, ba tare da wani abin zargi ba.

Babachir: Buhari bai so takarar Osinbajo ba

An rahoto Babachir Lawal, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa Yemi Osinbajo ya fafata da Bola Tinubu wajen neman tikiti.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ce marigayin ya ga rashin dacewa da kuma girmama dadaddiyar alakar da ke tsakaninsu.

Babachir Lawal ya kara da cewa, Buhari na ganin hakan a matsayin babban rashin ɗa'a da cin fuska ga Tinubu, wanda shi ya kawo Osinbajo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng