Yan ta'adda
Yan sanda sun yi nasarar kama mutum 25 da ake zargi da aika muggan laifukan ƴan bindiga a jihar Neja, kwamishinam ƴan sanda ya ce sun fara bada bayanai.
Jama'a sun yi zanga-zanga a garin Goningora da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna, sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai masu a daren Laraba.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai sabon hari a jihar Zamfara. Miyagun 'yan bindigan sun shiga har cikin masallaci sun sace masallata.
Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji (OPHD) ta sanar da samu nasara kan yadda ta'addan da suka addabi jihar Zamfara da ke shiyyar Arewa maso Yamma.
Ganin yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta'azzara, Sheikh Aminu Daurawa ya ba gwamnatin Shugaba Tinubu satar amsa, kan hanyar kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
A wani kazamin rikici da ya barke a Zamfara, kungiyar Ado Allero ta kashe akalla manyan ‘yan bindiga biyar da mayakan su 48. Yan bindiga na neman Allero ruwa a jallo
An kashe ‘yan bindiga da dama a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ke gaba da juna a kusa da Mada hanyar Gusau da karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
An ruwaito yadda 'yan ta'adda suka kai sabon hari a Kaduna bayan da aka kashe shugabansu a wani yankin jihar. An jima ana samun hare-hare a jihar Kaduna.
Mayakan kunhiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram sun sake kai hari kan turakun wutar lantarki a jihar Yobe. Maharan sun yi barna wacce ta sa aka shiga duhu.
Yan ta'adda
Samu kari