Bayan Jami’an Sun Kashe Shugabannin ’Yan Bindiga, Tsageru Sun Afkawa Mutane a Kaduna

Bayan Jami’an Sun Kashe Shugabannin ’Yan Bindiga, Tsageru Sun Afkawa Mutane a Kaduna

  • Rahoton da muke samu daga jihar Kaduna ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka kai sabon hari a jihar
  • An hallaka mutum daya tare da yin garkuwa da mutane da dama baya ga jikkata wasu adadi masu yawa
  • Jihohin Arewa masu Yamma na yawan fuskantar hare-hare daga tsagerun ‘yan bindigan da ke addabar yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kaduna - An ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan Busa da ke unguwar Doka a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna, inda suka kashe mazauna unguwar biyu tare da yin garkuwa da mutane 16 a daren ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Babban abin kunya: An kama matashi da laifin sace motar surukinsa, ya siyar N230,000

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce mutane biyar ne suka samu munanan raunuka, wanda a halin yanzu suke jinya a wani asibitin da ba a bayyana ba a yankin.

'Yan bindiga sun yiwa kisan gilla a Kaduna, sun sace jama'a
Yadda tsageru suka yi kisan gilla a Kaduna | Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Wannan dai ya biyo bayan murnar kashe Isyaku Boderia, wani dan bindiga a yankin, wanda aka ce ya shirya wasu manyan hare-hare da suka hada da sace 'yan matan makarantar Yauri da na Jami'ar Greenfield.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe ‘yan ta’adda a Kaduna

Hakazalika, an ce shi ya kitsa yadda aka kutsa makarantar horas da sojoji ta Najeriya kana ya yi garkuwa da wasu jami’ai tare da kashe manoma da mazauna kauye ba adadi.

Dakarun runduna ta daya ta sojojin Najeriya sun kashe dan bindigan nan mai suna Boderi a ranar Laraba a yankin Bada/Riyawa a karamar hukumar Chikun da Igabi a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mazaunin Abuja bayan karbar naira miliyan 20, sun kuma yi barazanar kashe wasu

Sojojin sun yiwa Boderi da mukarrabansa kwanton bauna ne tare da kawar da su a doron duniya bayan wani kazamin artabu da suka yi, Sahara Reporters ta ruwaito.

Sabon hari bayan kisan shugabannin ‘yan bindiga

Sai dai kuma a daren Juma’ar da ta gabata, ‘yan bindiga sun sake kai hari Gidan Busa, inda suka yi barna ba kakkautawa, tare da kashe mutum biyu da kuma yin garkuwa da akalla mutane 16 mazauna yankin.

Majiyar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare lokacin da mutanen kauyen ke barci mai nauyi cikin dare kamar yadda aka saba.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga rundunar ‘yan sandan jihar ko wata hukumar tsaro da ke yankin.

Hakazalika, kokarin jin ta bakin kakakin rundanar ‘yan sandan jihar ya ci tura, domin bai amsa wayar da aka yi masa ba, kana bai yi martani ga sakon kar ta kwana da aka aike masa ba.

Kara karanta wannan

Yan daba sun yi yunƙurin kutsawa kasuwar Jos don satar kayan abinci, jami'an tsaro sun dauki mataki

An kashe shugaban 'yan bindiga a Sokoto

A wani labarin, an kashe wani dan ta'addan da ake zargin shugaban tsageru a wani yankin jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da bayyana bukatar wanzuwar zaman lafiya a kasar.

A cewar 'yan sanda, an kuma kwato wasu muggan makamai a hannun dan ta'addan, ciki har da bindiga kirar AK47.

Asali: Legit.ng

Online view pixel