Mayakan Boko Haram Sun Tafka Sabuwar Barna a Jihar Yobe

Mayakan Boko Haram Sun Tafka Sabuwar Barna a Jihar Yobe

  • Mayaƙan Boko Haram sun sake jefa jihohin Yobe da Borno cikin duhu bayan sun lalata turakun da ke ɗauko wutar lantarki daga jihar Gombe
  • Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da hakan ta ce mayaƙan sun yi amfani ne da abubuwan fashewa wajen lalata turakun wutar lantarkin
  • Sake lalata turakun wutar lantarkin ma zuwa ne ƴan watanni kaɗan bayan an lalata su a cikin watan Disamban 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta ce wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun sake lalata wasu turakun wutar lantarki masu ƙarfin 330 KVA a jihar.

Rundunar ta ce lamarin jefa mazauna jihohin Yobe da Borno cikin halin duhu kamar yadda aka taɓa samun irin hakan a watannin baya, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ɗaliban fitacciyar jami'ar Arewa bisa zargin kashe rayukan bayin Allah

Maharan Boko Haram sun kai hari a Yobe
Maharan Boko Haram sun lalata turakun witar lantarki a Yobe Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Twitter

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Asabar, 24 ga watan Nuwamba a birnin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulkarim ya ce turakun wutan suna ɗauko wutar lantarki ne daga jihar Gombe zuwa jihohin Yobe da Borno, rahoton Aminiya ya tabbatar.

Ta wacce hanya suka lalata turakun?

Ya ce maharan sun yi amfani ne da abubuwan fashewa wajen lalata turakun da suka ɗauko wutar lantarkin a safiyar ranar Asabar.

A kalamansa:

"Waɗanan turakun wutar lantarkin suna a kusa da ƙauyen Kasaisa da ke ƙaramar hukumar Damaturu a Jihar Yobe.
"Wannan sabuwar ɓarna ta lalata turakun da ke ɗauke da wayoyin samar da hasken wutar lantarkin ya jefa mazauna jihohin biyu cikin duhu."

Wannan harin da aka kai kan turakun dai shi ne karo na biyu cikin watanni uku.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

A watan Disamba mahara sun lalata turakun wutar lantarkin, sai dai an gyara a watan Janairu, kafin yanzu da maharan suka sake lalata su.

Ƴan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun halaka mutum huɗu ciki har da soja ɗaya a wani harin kwanton ɓauna da suka kai a jihsr Borno.

Ƴan ta'addan sun kai harin ne a kan titin hanyar Gwoza Limankara mai nisan kilomita 134 talatin daga birnin Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel