'Yan Ta'adda Sun Ji Jiki da Dakarun Sojoji Suka Farmake Su a Plateau

'Yan Ta'adda Sun Ji Jiki da Dakarun Sojoji Suka Farmake Su a Plateau

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'adda da sauran miyagu a jihar Pleateau domin samar da tsaro
  • Sojojin na rundunar Operation Enduring Peace, sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama bayan sun kai farmaki a maboyarsu
  • Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar kwato makamai daga hannun 'yan ta'addan bayan sun fatattake su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Dakarun rundunar "Operation Enduring Peace" sun kashe aƙalla mutane shida da ake zargi 'yan ta'adda a jihar Plateau.

Sojojin sun kuma samu nasarar kwato bindigogin da aka ƙera a cikin gida a jerin samamen da suka kai a faɗin jihar Plateau.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Plateau
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Mai magana da yawun rundunar soji ta "Operation Enduring Peace", Chinonso Oteh, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun cafke jami'an tsaro da ke safarar makamai ga 'yan ta'adda

Yadda sojoji suka farmaki 'yan ta'adda

Ya ce an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 26 ga Yuni zuwa 2 ga Yuli a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu da kuma Barkin Ladi.

Kakakin ya ƙara da cewa hare-haren sun ginu ne bisa rahotannin sirri game da ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da ke gudanar da ayyukansu.

Oteh ya ce dakarun Sashe na 6 sun ƙaddamar da samame a ranar 26 ga Yuni a yankin Gero Highground da ke Jos ta Kudu biyo bayan rahotannin "ayyukan assha da dama" da mutanen da ake zargi 'yan ta'adda ne ke yi a yankin.

Sojoji sun yi gumurzu da 'yan ta'adda

A cewarsa, dakarun sun fuskanci harbi yayin da suke kusantar matattarar da ake zargi, inda ake zargin maharan sun yi amfani da dabbobi a matsayin garkuwa.

"Zuwa kai dauki a kan lokaci ya tilasta wa 'yan ta'addan ja da baya. Dakarun sun bi sawun 'yan ta'addan da ke gudu, sun kashe wasu daga cikinsu, kuma sun ci gaba da bincike a yankin domin tarwatsa matattararsu."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu bayan kai hari a Katsina

- Chinonso Oteh

Sojojin ba su bayyana takamaiman adadin 'yan ta'addan da aka kashe yayin wannan samamen ba nan da nan.

Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda kwanton bauna

Sojojin sun kuma ce dakarun da ke aiki bisa bayanan sirri sun yi wa mutanen da ake zargi 'yan ta'adda ne kwanton bauna a ranar 30 ga Yuni a kewayen tsaunin Rafin Bauna da Gero da ke Jos ta Kudu.

Mista Oteh ya ce an kashe mutane biyar da ake zargi 'yan ta'adda ne yayin da sauran suka tsere bayan an yi gumurzu.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ƙara da cewa binciken farko da kuma bayanai da aka samu daga mazauna yankin sun nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka kashe ɗin suna cikin jerin mutanen da sojoji ke nema ruwa a jallo saboda zarginsu da shirya hare-hare a Jos ta Kudu da kuma maƙwabciyarta karamar hukumar Bassa.

Sojojin sun kuma kai dauki wajen dakile wani harin da aka yi niyyar kaiwa ga cibiyar NIPSS da ke Kuru, inda aka kashe dan ta'adda daya.

Kara karanta wannan

Bayan shan wuta, mayakin ISWAP na kan kogi ya mika wuya ga jami'an sojoji

Sojoji sun cafke jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun cafke wasu jami'an tsaro da ake zargi da safarar makamai ga miyagu.

Sojojin sun cafke jami'an hukumar NSCDC guda biyu da jami'in hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa NCoS guda daya a jihar Enugu.

Dakarun sojojin sun gano tarin makamai daga hannun jami'an tsaron da ake zargi suna gada baki da masu aikata laifuffuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng