Mutane Sun Fusata, Sun Fito Zanga-Zanga Kan Hare-Haren 'Yan Bindiga a Jihar Arewa

Mutane Sun Fusata, Sun Fito Zanga-Zanga Kan Hare-Haren 'Yan Bindiga a Jihar Arewa

  • Wasu fusatattun mutane sun mamaye titi a garin Goningora da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna don yin zanga-zanga
  • Tsagerun 'yan bindiga sun kai hari garin a daren ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka biyu
  • Haka kuma, maharan sun yi garkuwa da mutane da dama tare da jikkata wasu, sannan suka kona motar yakin sojojin da suka yi kokarin dakile su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kaduna - Mazauna garin Goningora da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna, sun toshe babban titin Abuja zuwa Kaduna sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai garinsu.

An rahoto cewa maharan sun yi garkuwa da mutanen garin da dama yayin da wasu suka jikka a yayin harin na daren Laraba, 28 ga watan Fabrairu., Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 2 sun saduda yayin da suka mika wuya ga 'yan banga a Arewa, sun fadi dalili

Mazauna Kaduna sun fito sun yi zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga
Mutane Sun Fusata, Sun Fito Zanga-Zanga Kan Hare-Haren 'Yan Bindiga a Jihar Arewa Hoto: @NEWS_flp
Asali: Twitter

Fusatattun mazauna yankin sun mamaye unguwanni a safiyar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, inda masu motoci da dama suka makale.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin, inda masu motoci da matafiya da dama suka yi ciko-cirko.

Yadda 'yan bindiga suka farmaki al'ummar Goningora

An kuma rahoto cewa mutum biyu ciki harda wani 'dan kungiyar 'yan sa kai sun rasa ransu a harin.

Harin da aka kai garin Goningora na zuwa ne 'yan kwanaki bayan sojoji sun kashe wani kasurgumin 'dan bindiga, Boderi Isyaku, da wasu mayakansa a yankin na Chikun.

An rahoto cewa 'yan bindigar sun cinnawa wata motar yaki na sojoji wuta a lokacin da dakarun sojin suka yi yunkurin dakile su.

Ga bidiyon zanga-zangar a kasa:

An kama masu kera bindigu

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Benue ta kama wasu masu ƙera bindigu mutum uku a yankin Agu da ke ƙaramar hukumar Vandekiya ta jihar.

Kara karanta wannan

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin tarayya saboda abu 1, bidiyo ya bayyana

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Emmanuel Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar ƴan sandan jihar da ke Makurdi, babban birnin jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Ya bayyana cewa an samu nasarar cafke mutanen ne bayan an samu bayanan sirri kan ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel