An Yi Ƙazamin Karo Tsakanin Ƙungiyoyin Ƴan Bindiga, Ado Allero Ya Kashe Shugabannin Daba 5

An Yi Ƙazamin Karo Tsakanin Ƙungiyoyin Ƴan Bindiga, Ado Allero Ya Kashe Shugabannin Daba 5

  • Sabon rikici ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga a jihar Zamfara, an kashe mutane da dama tare da raunata wasu
  • Kungiyoyin daba na Dogo Bali da Kachallah Mai Yankuzu ne suka fara fadan, wanda har ta kai ga an kashe Dogo Bali, tare da kai harin ramuwa
  • Kachallah ya nemi taimakon Ado Allero, bayan dabobi da dama suka nemi kashe shi, inda Allero ya kashe manyan ƴan bindiga biyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Zamfara - A wani kazamin rikici da ya barke a jihar Zamfara, kungiyar Ado Allero ta kashe akalla manyan ‘yan bindiga biyar da mayakan su 48.

Rikicin ya faru ne a ranar Lahadi a kauyen Mada da ke Gusau, Yan Waren Daji, da Munhaye a karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sake kashe bakaken shugabannin ‘yan bindiga da yaransu

Dakarun sojojin Najeriya suna atisaye
Wannan dama ce ga sojojin Najeriya su kakkabe 'yan bindiga saboda rikicin da suke ciki. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Zagazola Makama, kwararren mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ya ruwaito cewa an fara rikicin ne da sanyin safiyar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutuwar Dogo Ali ta haifar da faɗan ƴan bindiga a Zamfara

Kungiyoyin Dogo Bali da Kachallah Mai Yankuzu ne suka fara fadan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka masu yawa, ciki har da Dogo Bali wanda ya kitsa harin na farko.

Wata majiyar leken asiri ta sanar da Makama cewa, mutuwar Dogo Bali ta sa wasu bangarorin da ke gaba da juna suka kai harin ramuwar gayya.

Wadannan kungiyoyi sun shiga cikin daji tun daga Hayin Alhaji zuwa Munhaye da ke cikin karamar hukumar Tsafe, inda suke neman daukar fansa kan mutuwar Bali.

Ado Allero ya kashe manyan shugabannin ƴan bindigar Zamfara

Da yake mayar da martani, Kachalla Mai Yankuzu ya nemi agajin Ado Allero, wanda ya yi gaggawar tara daruruwan mayaka, ya shirya arangama.

Kara karanta wannan

Bayan jami'an sun kashe shugabannin 'yan bindiga, tsageru sun afkawa mutane a Kaduna

Da isowarsu sansanin ‘Yan Ware da ke Tsafe, aka farmake su a wani mummunan harin kwantan bauna da dakarun Allero suka yi musu.

An dauki tsawon sa’o’i da dama ana gwabza kazamin fadan, inda kungiyar Ado Allero ta yi nasarar kashe fitattun ‘yan bindiga guda hudu: Dan Makaranta, Malam Gainaga, Malam Tukur, da Malam Jaddi.

Kungiyoyin ƴan bindiga sun taru don kai wa Allero farmaki

Dakarun Allero dai ba su tsaya nan ba, sun kuma kai hari a sansanin Alhaji Dan Nigeria, wani fitaccen shugaban ‘yan fashi da ke ‘Yan Ware.

Dan Najeriya da mayakansa sun yi gudu sun bar wurin, inda suka bar bindigu kirar AK47 sama da 150, wadanda kungiyar Allero ta kwace.

A yammacin ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, kungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban sun kai hari a sansanin Ado Allero da ke kauyen Munhaye amma ba su tarar da shi ba.

Sojoji sun samu damar kakkabe ƴan bindigar Zamfara

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Shugabannin 'yan fashin daji daga yankin yammacin Zamfara, wadanda suka hada da Yellow Jambros, Damina, Nagala, da Kawaji, suka isa Tsafe domin yin babbar arangama da Ado Allero.

Barkewar rikici tsakanin kungiyoyin 'yan fashi zai iya sojoji dama wajen kai farmaki don wargaza kungiyoyin 'yan bindiga na jihar Zamfara.

Sojoji sun kashe manyan shugabannin ƴan bindiga a Arewa

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe manyan shugabannin 'yan bindiga a jihar Kebbi.

Sojojin sun kashe Baldo da Baban Yara wadanda suka dade suna tafka barna a jihohin Arewa, kuna an kashe mabiyansu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel